logo

HAUSA

Dakarun gwamnati sun kawo karshen kawanyar da aka yi wa wani otel a Mogadishu

2022-08-21 15:49:14 CMG Hausa

Dakarun gwamnatin Somalia, sun kawo karshen kawanyar da mayakan Al-Qaeda suka yi wa wani otel dake Mogadishu babban birnin kasar, har na tsawon sa’o’i 30.

Wani kwamnadan tsaro ya shadawa kamfanin dillancin labarai na AFP da tsakar daren jiya agogon wurin cewa, jami’an tsaro sun kawo karshen kawanyar tare da kashe ‘yan bindigar, kuma ba a jin amon harbe-harben bindiga.

Ya ce babu karin bayani game da adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su, yana mai cewa, gwamnati za ta kira taron manema labarai a yau Lahadi. Ya kara da cewa, akwai bukatar tabbatar da kawar da duk wani abun fashewa da mai yuwuwa mayakan suka dasa.

Da farko dai, jami’an gwamnatin kasar sun ce fararen hula a kalla 13 sun mutu, wasu gommai kuma sun jikkata, bayan mayakan sun kai harin bama-bamai da harbe harben bindiga kan otel na Hayat da yammacin ranar Juma’a. Sai dai, jaridar Wall Street Journal ta Amurka ta ruwaito cewa, mutane sama da 20 sun rasa rayukansu, kamar yadda wasu ‘yan sanda 2 suka sanar da ita. (Fa’iza Mustapha)