logo

HAUSA

Rwanda na neman karin jarin kasar Sin kan ayyuka masu kare muhalli

2022-08-21 16:14:31 CMG Hausa

Gwamnatin Rwanda na kokarin jan hankalin karin jari daga kasar Sin kan ayyuka masu dacewa da raya muhalli, domin taimakawa kasar cimma burinta na raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba.

Darakta janar na hukumar kula da muhalli ta kasar Faustin Munyazikwiye, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a birnin Kigali cewa, Rwanda na fatan hada gwiwa da kasar Sin domin inganta kare muhalli mai dorewa.

Ya ce kasar na kiyaye muhalli da halittu ta hanyar amfani da fasahohin da suka dace. Kuma suna neman karin jari kan ayyukan raya muhalli daga kasar Sin, kasancewarta mai gogewa a bangaren fasahohin da suka dace da kare muhalli.

Ya kuma yi bayanin cewa, Rwanda da Sin na iya aiki tare wajen musayar dabaru a bangaren fasahohin da suka dace da kyautata muhalli, domin tabbatar da rage fitar da hayaki mai guba da sauran iftila’i, sakamakon sauyin yanayi.

Ya ce akwai masu zuba jari da dama daga kasar Sin dake zuwa domin zuba jari a kasarsa. Don haka, suna kira ga wadanda za su je zuba jari, su tabbata sun zuba jari a ayyukan da suke kare muhalli da za su bada gudunmuwa ga samun kyautatuwar muhalli mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)