logo

HAUSA

Masanin Masar: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Wani "Karfi Ne Dake Ingzia Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

2022-08-20 16:18:57 CMG Hausa

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa na kasar Masar ya bayyana cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, ta ingiza kokarin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, duba da irin gudummawar da shawarar ta bayar ga ci gaban Afirka.

Ezzat Saad, darektan hukumar kula da harkokin waje ta Masar, shi ne ya bayyana hakan, yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da aka yi da shi a baya-bayan nan, yana mai cewa, galibin kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Afirka, ciki har da Masar, abokan hadin gwiwar shawarar ce, kuma shawarar ta samar da alfanu da dama ga nahiyar Afirka, ciki har da inganta ababen more rayuwa a kasashen Afirka.

Saad ya ce, sabanin tallafin da wasu kasashen yammacin duniya ke bayarwa, wadanda galibi suka takaita ga taimakon raya kasa bisa wasu sharudda da suke gindayawa, akwai bambanci mai girma da taimakon da kasar Sin ke baiwa kasashen Afirka.

Ya kara da cewa, kasar Sin ba ta gindaya wasu sharudda, kuma tallafin da take bayarwa, na da nufin yakar talauci da samun ci gaba ga kasashen Afirka.

Ya kuma ci gaba da cewa, hakika kasar Sin ta ba da babban taimako dangane da tsare-tsare na samun ci gaba a kasashen Afirka da dama.

Saad ya yi imanin cewa, shawarar ta kunshi dukkan sassan da za su shafi kyakkyawar dangantaka tsakanin bangarorinta, kuma tana yin hulda da bangarorin da suka hada da hadin gwiwar tattalin arziki, da ababen more rayuwa, da sufuri, da mu'amalar cinikayya, da zamanantar da fasahar zamani, da masana'antu, da goyon baya da musayar al'adu.(Ibrahim)