Amurka Na Cin Zarafin Wasu Kasashen Duniya
2022-08-19 21:46:18 CMG Hausa
Duniya tamkar wani kauye ne da kunshi masu kudi da marasa shi. Mafi arziki kan ci zarafin matalauta har ma ya kwace dukiyoyin da suka mallaka. Wannan kauyen ita ce duniyarmu, kuma mafi arzikin ita ce kasar Amurka.
Wata rana a kwanaki 10 na tsakiyar watan Agustan bana, sojojin Amurka sun sake zuwa filin hakar mai a lardin Al Hasakah da ke arewa maso gabashin kasar Syria. Sun yi jigilar man da suka sata cikin goman manyan motocin dakon mai zuwa sansaninsu dake kasar Iraki, bayan da suka ketare iyakar kasashen 2 ba bisa doka ba. Wannan shi ne karo na 6 a watan Agustan bana da sojojin Amurka suka saci mai a Syria. Alkaluman gwamnatin Syria sun nuna cewa, a shekarar 2021 da ta gabata, Amurka ta kwace sama da kaso 80 cikin 100 na man fetur din da Syria ta hako. Sakamakon yadda sojojin Amurka ke kara satar man, ya sa tun daga ranar 7 ga watan Agustan bana farashin mai ya karu da 127% a Syria.
Baya ga haka kuma, sojojin Amurka sun kwace alkaman da Syria ke dogaro da su. Da ma Syria tana sayar da hatsi zuwa ketare. Yawan alkaman da ake nomawa a Syria a ko wace shekara, ya kai kusan ton miliyan 5, kana a kan sayar da kimanin ton miliyan 2 zuwa ketare daga Syria. Amma sakamakon sa baki ta fuskar aikin soja da sojojin Amurka suka yi a Syria ba bisa doka ba, ya sa Amurka ta fara kwace albarkatun Syria, lamarin da ya sanya jama’ar Syria da yawansu ya kai 90% tsunduma cikin yanayi na kangin talauci. An raba wasu fiye da miliyan 10 da muhallansu. Wani manomi a Al Hasakah ya ce, Amurka ta ce tana yaki da ta’addanci ne, amma abin da take yi, tamkar ta’addanci ne.
Munafuncin dodo ya kan ci mai shi. Amurka za ta kirbi abin da ta shuka. (Tasallah Yuan)