logo

HAUSA

Wadanda suka rasu sakamakon wutar daji a Aljeriya sun karu zuwa mutum 37

2022-08-19 13:28:09 CMG Hausa

Hukumar kare al’umma ta kasar Aljeriya ta ce, ya zuwa jiya Alhamis, adadin mutanen da suka rasu, sakamakon wutar daji da ta mamaye sassan tsaunukan dake lardunan Al Taref da Setif na gabashin kasar Aljeriya, sun karu zuwa mutum 37, kana ibtila’in ya raunata wasu mutanen 183.

Rahotanni na cewa, duk da an yi nasarar kashe kaso mai yawa na wutar, har yanzu jami’an kashe gobara, da jirage masu saukar ungulu na ci gaba da sintiri domin kandagarkin sake bullar wutar.  (Saminu Alhassan)