logo

HAUSA

Mai yiwuwa kamfanin Emirates ya dakatar da zirga zirgar jiragen sa zuwa Najeriya

2022-08-19 13:35:43 CMG Hausa

Kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates, ya sanar da shirinsa na dakatar da zirga zirgar jiragensa zuwa Najeriya tun daga ranar 1 ga watan Satumba dake tafe, a wani mataki na rage asara, bayan da ya gaza samun damar fitar da kudadensa da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 85 daga Najeriya.

Akwai dai yarjejeniyar da ta tanadi baiwa ’yan Najeriya damar sayen tikitin jiragen kamfanonin kasashen waje da kudin kasar Naira, kana babban bankin kasar CBN ya biya kamfanonin, da kwatankwacin cinikin su a dalar Amurka. To sai dai kuma, gaza karbar dala daga CBN, ya sa kamfanin Emirates yanke shawarar dakatar da sufuri a Najeriya, tare da alkawarin tallafawa fasinjojin sa da duk wata hanya, ta sauya tsarin tafiye tafiyen su gwargwadon iko.

Kamfanin jiragen saman mai helkwata a Dubai, ya ce akwai yiwuwar ya sake matsaya game da wannan mataki, idan har aka samu wani ci gaba cikin kwanaki masu zuwa, game da batun karbar dalar Amurka daga babban bankin Najeriya CBN.  (Saminu Alhassan)