logo

HAUSA

Daliban kasar Ghana 86 sun samu gurbin karatu na jakadan kasar Sin

2022-08-18 11:11:39 CMG Hausa

Cibiyar Confucius ta koyar da yare da al’adun kasar Sin dake jami’ar Ghana, ta ce wasu daliban kasar Ghanan su 86, sun samu gurbin karo ilimi a makarantun kasar Sin, bisa kwazon su a fannin koyon Sinanci. Cibiyar ta ce daliban sun samu guraben karo ilimin ne na jakadan kasar Sin na bana.

Da yake tabbatar da hakan, daraktar bangaren Sin ta cibiyar ta Confucius dake jami’ar Ghana madama Chu Beijuan ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bayan tantance dalibai masu yawa, an zabo dalibai mafiya hazaka daga wasu jami’o’i, da makarantun firamare, da na gaba da firamare dake kasar, domin cin gajiya daga wannan dama.

Chu ta kara da cewa, cikin shekaru da dama da suka gabata, sha’awar harshen Sinanci na karuwa kwarai a tsakanin daliban kasar Ghana, yayin da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ke kara fadada.

Ta ce baya ga damar karo karatu a Sin da harshen Sinanci ke baiwa daliban kasar Ghana, yana kuma taimaka musu wajen samun guraben ayyukan yi a kamfanonin kasar Sin da dama dake Ghana.

An kafa cibiyar Confucius ta koyar da yare da al’adun kasar Sin dake jami’ar Ghana ne a shekarar 2013, kuma ya zuwa yanzu, ta horas da dubun dubatar daliban kasar Ghana a matakai daban daban, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasa musayar al’adu tsakanin Sin da kasar Ghana.  (Saminu Alhassan)