logo

HAUSA

Najeriya: An tsaurara matakan tsaro a jihar Lagos sakamakon barazanar tsaro

2022-08-18 11:21:39 CMG Hausa

Kwamishinan ’yan sanda na jihar Lagos dake kudancin Najeriya Abiodun Alabi ya ce, za a aiwatar da karin matakan tsaro a sassan jihar domin dakile duk wani yunkuri na kaddamar da harin ta’addanci.

Alabi wanda ya bayyana hakan, yayin taron majalissar tsaron jihar na jiya Laraba, ya ce ’yan sanda da sauran jami’an tsaro dake birnin Ikko, za su kafa shingayen bincike, domin tabbatar da mahara ba su samu damar yin kutse cikin jihar ba.

Duk da cewa bai yi karin haske kan girman barazanar tsaron ba, amma jami’in ya yi kira ga al’ummar jihar, da su gabatar da sahihan bayanan duk wasu ayyukan karya doka, ga ’yan sanda da sauran jami’an tsaro dake jihar. (Saminu Alhassan)