logo

HAUSA

Kayayyaki kirar kasar Sin suna haskaka gasar cin kofin duniya ta Qatar

2022-08-18 20:03:37 CMG Hausa

Za a gudanar da gasar cin kofin duniya ta Qatar tun daga ranar 20 ga watan Nuwanba, zuwa ranar 18 ga watan Disamba a bana. A halin yanzu, ana shiga matakin karshe na shirya gudanar da gasar a fannoni daban daban.

Kamfanonin kasar Sin da dama wadanda suka samar da kayayyakinsu, suna tabbatar da gudanar da gasar, tare da samar da hidimomi a fannonin gina filayen kwallon kafa, da zirga-zirgar motoci, da fasahohin sadarwa, da kayayyakin yau da kullum da sauransu, kayayyaki kirar kasar Sin suna haskaka gasar cin kofin duniya ta Qatar.

Filin wasa na Lusail, muhimmin filin wasa ne da za a yi amfani da shi wajen gudanar da gasar cin kofin duniya na Qatar, inda za a yi wasanni 10 na gasar ciki har da wasan karshe na gasar. Filin wasan shi ne mafi girma a kasar Qatar a halin yanzu. Reshen kasashen waje na kamfanin CRCC na kasar Sin shi ne ya gina wannan filin wasan, kuma wannan ne aikin gina filin wasa na gasar cin kofin duniya na farko da kamfanin Sin ya aiwatar, inda a baya kamfanonin kasashen Amurka da Turai ne kadai suka gudanar da irin wannan aiki.

Filin wasa na Lusail da kamfanin CRCC na kasar Sin ya gina, fili wasa ne mafi girma dake kunshe da fasahohin zamani mafi kan gaba da kamfanin Sin ya gina a kasashen waje. Mataimakin manaja na reshen kasashen waje na kamfanin CRCC Li Chongyang ya bayyana cewa,“Filin wasa na Lusail, filin wasa ne da aka yi amfani da ma’aunin hukumar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA, wajen gina shi, kunshe da fasahohin zamani mafiya girma, kuma mai samun tsarin sarrafawa mafi sarkakiya. A yayin da ake gina filin wasan, kasancewar kamfanin Sin ne ya aiwatar da ginin, an yi amfani da fasahohin Sin, da kayayyakin kirar kasar Sin kan aikin ginin. Aikin da aka gama ya shaida fasahohin zamani, da na’urori masu kyau da kuma karfin kamfanin Sin.”

Game da aikin gina filin wasa na Lusail mai inganci da kamfanin Sin ya gama cikin nasara, bangarori daban daban na kasar Qatar sun nuna yabo ga aikin. A shekarar 2020, bankin tsakiya na kasar Qatar, ya fitar da kudin Rial 10 wanda zane-zanen dake kan kudin ya kunshi filin wasa na Lusail, wannan ne karo na farko da filin wasan da Sin ta gina ya fito a kan kudin kasar Qatar. Babban sakataren kwamitin shirya gasar cin kofin duniya na kasar Qatar Hassan Al Thawadi ya bayyana cewa,“Za a gudanar da wasan karshe na gasar cin kofin duniya na Qatar a filin wasa na Lusail, filin wasan shi ne mafi girma, a cikin dukkan filayen wasa da za a gudanar da wasannin gasar a wannan karo, wanda ke iya daukar masu kallo dubu 80. Ana iya gama gina irin wannan filin wasa mai fasahohin zamani, wannan ya shaida karfin kamfanin Sin wajen gina babban filin wasa. Dukkan masu kallo da za su shiga filin wasan don kallon wasannin gasar cin kofin duniya ta Qatar, musamman masu kallo daga kasar Sin, ya kamata su jinjinawa ma’aikatan ginin filin wasan na kasar Sin.”

Ban da filin wasa na Lusail, kamfanonin Sin sun shiga ayyukan gina filayen wasa da za a yi amfani da su, wajen gudanar da gasar cin kofin duniya ta Qatar, kana akwatunan ajiye kaya da ake amfani da su yayin gina filayen wasan guda 974, su ma akwatuna ne kirar kasar Sin.

A fannin sufuri, kasar Qatar tana kokarin rage fitar da iskar dumamar yanayi, da sa kaimi ga inganta tsarin sufurin jiragen karkashin kasa, da bas da sauransu, ta hakan jama’ar kasar, da masu sha’awar wasan kwallon kafa, da masu kallon gasar cin kofin duniya za su iya hawa jiragen karkashi kasa, da bas a yayin gasar cin kofin duniya na Qatar.

Kana kasar Qatar ta kafa wata tawagar ayarin motoci masu amfani da karfin lantarki fiye da 700, don gudanar da ayyukan daukar masu kallo a yayin gasar cin kofin duniya ta Qatar, inda yawansu ya kai kashi 25 cikin dari, bisa adadin motocin da za a yi amfani da su wajen bada hidima a yayin gasar.

Motoci kirar kasar Sin, su ma sun shiga gasar cin kofn duniya na Qatar. A shekarar 2020, kamfanin Yutong na kasar Sin ya samu iznin gudanar da aikin samar da hidimar sufurin motoci a yayin gasar, inda kasar Qatar za ta shigar da motocin da kamfanin Yutong na kasar Sin ya kera kimanin 1500, ciki har da motoci masu amfani da karfin lantarki 888, don samar da hidima a yayin gasar cin kofin duniya ta Qatar. Domin yanayin kasar Qatar yanani ne mai zafi sosai, da kuma yanayin hamada a kullum, kamfanin Yutong na kasar Sin ya kera, da kyautata samfurin motocin da za a samar da su zuwa kasar Qatar don dacewa da yanayin kasar, da tabbatar da bada hidima a yayin gasar. Manajan reshen kasar Qatar na kamfanin Yutong Wang Zhengbin ya bayyana cewa,“Ana sa ran za a yi amfani da motoci kimanin 1500, wadanda kamfanin Yutong ya samar wajen bada hidimar sufuri, a yayin gasar cin kofin duniya ta Qatar, wadanda za su dauki jami’an gwamnati, da jami’an kwamitin shirya gasar, da wakilan kafofin watsa labaru, da kuma masu kallo zuwa filayen wasan gasar. A cikin motocin 1500, akwai guda 888 masu amfani da karfin lantarki, wannan ne karo na farko da za a yi amfani da motoci masu amfani da karfin lantarki da yawa a yayin babbar gasar wasanni ta duniya.

Ban da samar da motoci, kamfanin Yutong ya daddale yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da bangaren kasar Qatar, da kafa kamfanin kera motoci masu daukar fasinja dake amfani da karfin lantarki, a yankin ciniki cikin ‘yanci na kasar Qatar, don koyar da fasahohi, da horar da kwararru a kasar.

Kamfanin ya tsaida shirin fara kera motoci a watan Nuwanba na shekarar 2023, inda za a samar da motoci masu amfani da karfin lantarki 500 zuwa 1000 ga kasar Qatar a kowace shekara.”

Bangaren Qatar dake hadin kai da kamfanin Yutong, kamfanin sufuri ne na kasar Qatar mai suna Mowasalat, yana kuma fatan za a fadada hadin gwiwa tare da kasar Sin a nan gaba. Babban shugaban gudanawar kamfanin Ahmed Al Obaidly ya bayyana cewa,“Kamfanin Yutong, yana daya daga cikin manyan kamfanonin samar da motoci masu daukar fasinja na duniya. Muna yin hadin gwiwa tare da kamfanin Yutong wajen samun sakamako mai kyau. Bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa, da kyautata samfurin motoci tare, don sa motoci su dace da yanayin kasarmu. A nan gaba, ina fatan za a kara fadada hadin gwiwa tare da kamfanin Yutong, don samun ci gaba tare.”

Abubuwan da dama dake shafar gasar cin kofin duniya na Qatar, su ne masu kirar kasar Sin, ciki har da ayyukan sadarwa a filayen wasa, da na’urorin sadarwa na yanar gizo dake cibiyar sarrafa filayen wasan gasar, da shingen da aka ajiye a filayen horaswa, da tuta da riga da kayayyaki masu nasaba da gasar cin kofin duniya ta Qatar da sauransu.

Ana iya cewa, kayayyakin kirar kasar Sin, za su haskaka gasar cin kofin duniya ta Qatar a fannonin gina filayan wasa, da tabbatar da gudanar da gasar, da bada hidima a yayin gasar, da samar da kayayyakin dake nasaba da gasar da sauransu. (Zainab Zhang)