logo

HAUSA

Babu Nasara Ga ’Yan Awaren Taiwan

2022-08-18 19:37:45 CMG Hausa

Bisa dukkanin shaidu da dalilai na zahiri, ’yan a waren yankin Taiwan na kasar Sin, da masu mara musu baya daga ’yan siyasar kasashen yamma, ba su da wani buri da ya wuce jefa Taiwan cikin yanayi na rudani.

Lura da hakan ne ma ya sanya mahukuntan kasar Sin dukufa matuka, wajen yin aiki kafada da kafada da masu burin ci gaban tsibirin Taiwan, wajen shawo kan duk wasu batutuwan da suka shafi sake dinkuwar yankin da babban yankin kasar Sin cikin lumana. Ko shakka babu, aiwatar da wannan manufa ta hanyar nacewa salon kasa daya tsarin mulki biyu, shi ne mataki mafi dacewa na dinkuwar kasar Sin cikin ruwan sanyi, amma kuma duk da haka, ya kamata masu son gurgunta wannan manufa su san cewa, gwamnatin kasar Sin ba za ta bar duk wata kafa ta cimma nasarar ’yan a ware ba.

Bisa goyon bayan daukacin al’ummun kasar Sin, da kudurorin MDD masu nasaba da hakan, da ma goyon bayan sauran sassan kasa da kasa, batun dinkuwar yankin Taiwan na da tushe na dokar kasar Sin, da ma dokokin cudanyar kasa da kasa. Kaza lika bangarorin da suka ki amincewa da hakan, suna kokari ne na tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da yunkurin gurgunta moriyar kasar da ikon mulkin kanta.

Sanin hakan ne kuma ya sanya gwamnatin kasar Sin ta shirya tsaf, domin tunkarar duk wani shiri na amfani da batun Taiwan, don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar. Hakan tamkar kashedi ne, da jan kunnen masu ganin za su iya keta hurumin ikon mulkin kai na kasar Sin. Domin kuwa Sin na da ikon amfani da dukkanin hanyoyi mafiya dacewa, na kare kai daga barazanar makiya.

Bahaushe kan ce “Idan kunne ya ji jiki ya tsira”, wato dai bayanai da mahukuntan kasar Sin ke fitarwa, da matakai na zahiri da gwamnatin kasar ke dauka, na tabbatar da cewa, ’yan a waren yankin Taiwan, da masu mara musu baya daga ’yan siyasar kasashen yamma, ba za su taba yin nasarar cimma mummunar manufar su ba! (Saminu Hassan)