logo

HAUSA

Ana Kulle Kaya A Manyan Shagunan Zamani Da Makulli A Amurka

2022-08-18 21:53:43 CMG Hausa

Ko ana kulle kaya masu araha ma a manyan shagunan zamani da makulli a kasar Amurka? Ko barayi sun saci kayayyaki sau hudu a shago guda a dare guda? Wadannan abubuwa sun abku ne a birnin New York, birni mafi girma a Amurka. Wadannan su ne irin matsalolin da Amurka ke fuskanta.

Baya ga karuwar yawan laifuffukan satar kaya, nuna karfin tuwo ta hanyar amfani da bindiga da laifuffukan nuna tsana su ma suna adabar Amurkawa. Gidan rediyon NPR na Amurka ya ruwaito a kwanan baya cewa, wasu mutane ba su son ci gaba da ayyukan da suke yi a titin Wall Street sakamakon karuwar laifuffuka, don haka shugabannin kamfanoninsu sun taimaka musu wajen magance irin fargabar tsoron da suke yi.

Amurka ta dade tana fama da dimbin laifuffuka a duniya. Yanzu haka barkewar cutar COVID-19 da hauhawar farashin kaya da sauransu sun tsananta matsalar da Amurka ke fuskanta.

A watan Yuli kawai, an sayar da bindigogi fiye da miliyan 1 da dubu 200 a Amurka, adadin da ya kafa tarihi. Karin Amurkawa suna sayen bindiga domin kare kansu, yayin da karin mutane suke kara damuwa kan tsaron lafiyarsu. Ko Amurka mafi karfi a duniya za ta iya daidaita matsalar da take fuskanta? Idan ba ta iya kare lafiyar jama’arta ba, to, ta yaya za ta kare jama’ar sauran kasashe? (Tasallah Yuan)