logo

HAUSA

Najeriya: An kaddamar da kwamitin yaki da cutar malaria

2022-08-17 10:22:09 CMG Hausa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yaki da cutar zazzabin cizon sauro ko Malaria. Kwamitin na EMC na karkashin tsarin hadin gwiwar gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma sassa masu zaman kansu, yana kuma kunshe da mambobi 16.

Yayin kaddamar da shi a jiya Talata, shugaba Buhari ya ce baya ga inganta rayuwar al’umma, da kyautata kiwon lafiya, da walwalar al’umma, shirin yaki da Malaria a Najeriya zai yi tasirin gaske, wajen kyautata tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.

Buhari ya ce kwamitin EMC zai samar da dandali da zai jawo karin kudaden gudanarwa, domin ayyukan kandagarki da dorewar nasarorin da ake samu a kasar a fannin, matakin da zai kai Najeriyar ga kawar da cutar malaria baki daya.

Shugaban na Najeriya ya koka game da yadda dadaddiyar cutar ta zamewa kasar alakakai, inda ya hakaito rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO na bara, wanda ya ayyana Najeriya a matsayin wadda ke dauke da kaso 27 bisa dari na daukacin wadanda suka sha fama da cutar Malaria, ita ce kuma mai kaso 32 bisa dari na jimillar mutanen da cutar ta hallaka a duniya baki daya a shekarar ta 2021. (Saminu Alhasan)