Ci gaban Kasar Sin Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata
2022-08-17 09:15:24 CMG Hausa
A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta sami gagarumin ci gaba a fannonin tattalin arziki da, binciken sararin samaniya, kirkire-kirkire da inganta muhalli da zaman rayuwar jama’a da sauransu
Daga shekarar 2012 zuwa 2022, karfin tattalin arzikin kasar Sin ya kai wani sabon matsayi, ma’aunin GDPn kasar ya kai Yuan triliyan 114, adadin da ya kai kashi 18 bisa dari na karfin tattalin arzikin duniya, wanda bai wuce kashi 11.4 bisa dari ba a shekarar 2012.
A wadannan shekaru, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 bisa dari ta fuskar bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wadda ta kasance babbar kasar dake taimakawa karuwar tattalin arzikin duniya. Kana ta yi nasarar warware babbar matsalar fama da kangin talauci, wadda ta damu jama’ar Sin cikin dubban shekaru da suka gabata. Mazauna kauyuka kimanin miliyan 98.99 sun fita daga kangin talauci. Adadin kauyukan da suka sauya zuwa birane, ya karu daga 53.1% zuwa 64.7%. Mazauna kauyuka kimanin miliyan 180 sun kaura zuwa birane.
A fannnin kirkire-kirkire kuwa, kasar Sin ta bayar da muhimmanci ga fannin kirkire-kirkire don tabbatar da ci gaban kasa, matsayin kasar Sin a kasashen duniya da suka fi mai da hankali kan harkokin kirkire-kirkire, ya tashi daga matsayi na 34 zuwa matsayin 12, kana Sin ta zama kasa daya tilo da ta samu saurin bunkasuwa babu kakkautawa a wannan fanni.
Haka kuma kasar Sin ta yi nasara a kokarin da take yi na gina tashar binciken sararin samaniyar Tianhe, matakin dake nuna gagarumin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin binciken sararin samaniya. Haka kuma, fasahohin jiragen kasa masu saurin gaske, da tsarin samar da wutar lantarki da fasahar sadarwa, da sabuwar fasahar samar da wutar lantarki mai amfani da makamashin nukiliya, dukkansu suna kan gaba a duniya.
Bugu da kari, muhallin kasar Sin ya kyautatu matuka cikin wadannan sheakru 10. adadin makamashi masu tsabta da aka yi amfani da su bisa dukkan makamashin da aka yi amfani da su a kasar Sin, ya karu daga 14.5% zuwa 25.5%. Yawan itatuwan da aka shuka a cikin kasar Sin, ya kai kashi 1 bisa uku na dukkanin itatuwan da aka shuka a fadin duniya, lamarin da ya sa, adadin hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da kasar Sin take fitarwa ya ragu matuka.
Daga shekarar 2012 zuwa 2022, yawan kudin shiga na al’ummomin kasar Sin na ci gaba da karuwa, rayuwar jama’a ya inganta sosai, wannan ya sa, karfin yin sayayya na jama’ar kasar Sin ya karu matuka. A shekarar 2021, darajar jimillar kayayyakin yau da kullum da aka sayar a cikin kasar Sin, ta kai yuan triliyan 44.1, kwatankwacin dallar Amurka kimanin tirliyan 6.58, adadin da ya ninka sau 1.1 idan aka kwatanta da na shekarar 2012, wato adadin ya karu da 8.8% a ko wace shekara. Bugu da kari, sayar da kayayyaki ta yanar gizo, da harkokin kasuwanci a tsakanin ’yan kasuwa na kasar Sin da na kasashen waje ta yanar gizo, da kuma biyan kudade da wayar salula, da sauran sabbin fasahohi da tsare-tsare na ci gaba da karuwa.
Bangaren lafiyar mata da kananan yara, shi ne muhimmin tushen tabbatar da lafiyar dukkanin al’umma. Babban mizanin lafiyar mata da kananan yara ya hada da yawan mata masu ciki dake mutuwa yayin haihuwa, da yawan yara ‘yan kasa da shekaru 5 da jarirai dake mutuwa.
Bugu da kari, cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta bullo da tsarin ilimin gaba da sakandare mafi girma a fadin duniya. An ci gaba da kyautata hanyoyin koyarwa, da tsarin gudanar da ayyuka a manyan makarantu, da inganta yanayin koyo a manyan makarantu, domin zakulo masu hazaka da kwarewa da kuma kara karfin yin kirkire-kirkire.
A cikin wadannan shekaru wato 2012 zuwa 2022, bangaren zirga-zirga na kasar Sin ya bunkasa sosai, lamarin da ya inganta jin dadin zaman al’umma. Kuma, alkaluman aikin zirga-zirga na layukan dogo, da manyan hanyoyi, da jiragen ruwa da kuma na jiragen sama da dai sauransu, suna kan gaba a duniya cikin shekaru da dama da suka gabata, hakan ya sa, kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen dake da yawan zirga zirgan ababen hawa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)