logo

HAUSA

Tawagogin aikin wanzar da zaman lafiya sun ci gaba da aiki a Mali

2022-08-17 11:02:11 CMG Hausa

Babban mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya ce tawagogin dakaru dake aikin karba-karba na wanzar da zaman lafiya a kasar Mali, sun koma bakin aiki, bayan da gwamnatin kasar ta dakatar da ayyukan su har tsawon wata guda.

Dujarric ya ce tawagar dakarun kasar Bangladesh ce ta fara ayyukan ta a kasar tun daga ranar Litinin, kuma nan daga kadan, tawagar dakarun kasar Senegal mai kunshe da dakaru kimanin 400, za ta karbi aikin na karba karba.

Jami’in ya kara da cewa, "Muna maraba da kokarin da gwamnatin rikon kwaryar Mali, da dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya masu aiki a kasar ke yi. Muna kuma jinjinawa sama da kasashe 60, da ke samar da sojoji da ’yan sanda masu aikin na wanzar da zaman lafiya a Mali.

(Saminu Alhassan)