logo

HAUSA

Raila Odinga zai kalubalanci sakamakon babban zabe a kotu

2022-08-17 11:00:38 CMG Hausa

Shugaban ’yan adawa, kuma daya daga manyan ’yan takarar shugabancin kasar Kenya, a babban zaben kasar da aka sanar da sakamakon sa a ranar Litinin Mr. Raila Odinga ya musanta shan kaye, tare da shan alwashin garzayawa kotu, domin kalubalantar sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar, wanda ya ayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin wanda ya yi nasara.

Odinga mai shekaru 77 da haihuwa, ya yi takarar shugabancin kasar Kenya ne a karo na 5, karkashin jam’iyyar One Kenya Coalition. Ya kuma shaidawa dandazon magoya bayansa cewa, ko alama bai gamsu da sakamakon zaben da aka bayyana ba.

Ya ce hukumar zaben kasar IEBC, ta sabawa kundin mulkin Kenya, ta kuma yi watsi da tanadin cimma matsaya da aka amincewa, inda ta ayyana Mr. Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben. Don haka a cewarsa, tsagin da yake wakilta zai garzaya kotu domin bin bahasi.

Magoya bayan Mr. Ruto mai shekaru 55 da haihuwa, sun yi ta gudanar da shagulgulan murnar nasarar da ya samu, a yankunan da yake da rinjayen magoya baya, yayin da tsagin magoya bayan Odinga suka rika bayyana bacin ran su ga sakamakon zaben.

Hukumar zaben kasar Kenya ta ce Mr. Ruto ya yi nasarar lashe zaben na ranar 7 ga wata ne da kuri’u miliyan 7.17, kimanin kaso 50.49 bisa dari na jimillar kuri’un da aka kada. (Saminu Alhassan)