logo

HAUSA

Dangantakar Sin Da Kasashen Afrika: Yabon Gwani Ya Zama Dole

2022-08-16 18:50:39 CMG Hausa

Kasashen Afrika na kara samun ci gaba da kara amfana daga kyakkaywar dangantakar moriyar juna dake tsakaninsu da kasar Sin. A wannan mako, kasar Habasha ta kaddamar da manyan ayyukan ci gaba guda biyu masu muhimmanci ga tattalin arziki da walwalar jama’a da suka hada da yankin ciniki cikin ’yanci na farko a kasar da kuma wani babban titin da ya fara daga shataletalen Alexander Puskin zuwa babban titin Gotera, dake birnin Addis Ababa.

A ko da yaushe, na kan ce dangantakar Sin da kasashen Afrika dangantaka ce ta zahiri da idanu ke iya gani, sannan al’umma kan amfana kai tsaye. Yankin masana’antu na Dire Dawa da tashar jiragen ruwa ta kan tudu da tashar jirgin kasa da ta hada Habasha da Djibouti ne suka hade, suka zama yankin na ciniki cikin ’yanci. Dukkan wadannan ayyuka ne da Sin ke da ruwa da tsaki wajen wanzuwarsu, wadanda kuma kasar za ta dade tana cin gajiyarsu. Yankin masana’antu na Dire Dawa kadai, zai taimaka wajen samar da ayyukan yi na kai tsaye da wanda ba na kai tsaye ba ga al’ummar kasar 40,000, baya ga wadanda ya samarwa aikin yi yayin da ake gininsa. Wannan yankin da ba za a taba raba nasararsa da taimakon kasar Sin ba, zai yi gagarumin taimako wajen habaka cinikayya tsakanin kasar da sauran kasashen Afrika musamman na gabashin nahiyar da saukaka jigilar kayayyaki da inganta rayuwar mazauna yankin da ma kai kasar ga cimma burinta na zama kasa mai matsakaicin kudin shiga zuwa shekarar 2025.

Kasar Habasha ta tsara burinta na zama cibiyar samar da kayayyaki da masana’antu na zamani a nahiyar Afrika, kuma kasar Sin tana iya kokarinta na ganin ta cimma wannan buri.

Har ila yau a jiya, kasar ta kaddamar da babban titin da ya fara daga shataletalen Alexander Puskin zuwa babban titin Gotera, a birnin Addis Ababa. Titi muhimmin aikin more rayuwar al’umma ne domin zirga-zirga ya shafi dukkan bangarorin rayuwa, kama daga zuwa aiki, asibiti, jigilar kayayyakin bukata, da dai sauransu.

Tabbas kasar Sin ta cancanci yabo. Hakika duk wanda zai soki dangantakar Sin da Afrika, to ba ya kaunar ganin ci gaban kasashen na Afrika, domin cikin lokaci kalilan da aka dauka na dangantakar bangarorin biyu, an samu dimbin nasarorin da suka amfanawa daukacin al’umma, wadanda tarin zuri’a masu zuwa, su ma za su ci gajiya.(Fa’iza Mustapha)