Tattalin arzikin Sin yana ci gaba da bunkasa yadda ya kamata
2022-08-16 10:44:12 CMG Hausa
Alkaluman kididdiga na gwamnatin kasar Sin sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar yana ci gaba da farfadowa, lamarin da ya kara imanin kasa da kasa kan tattalin arzikin kasar.
Alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta fitar jiya, sun nuna cewa, adadin GDP na kasar ya karu da kaso 2.5 bisa dari a rabin farko na bana bisa makamancin lokacin bara, wanda ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba yadda ya kamata.
Duk da cewa, ana fuskantar kalubale da matsaloli a fannoni daban daban, yanayin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai dorewa bai sauya ba, saboda gwamnatin kasar ta dauki matakai a jere a bangaren kandagarkin cutar COVID-19 da na raya tattalin arziki da kuma na tabbatar da tsaro yayin gudanar da ayyukan sana’o’i.
Ana cike da imani cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da farfadowa lami lafiya, kuma ci gaban Sin zai amfanawa ci gaban tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. (Jamila)