logo

HAUSA

Najib Ahmed: Kasar Sin har kullum ci gaba take

2022-08-16 14:38:56 CMG Hausa

Najib Ahmed, wani dan Najeriya ne wanda ya shafe kusan shekaru 10 yana karatu da zama a birane daban-daban na kasar Sin, inda ya samu digiri na biyu da na uku dukka a kasar Sin. Yanzu haka kwararren mai bincike ne a jami’ar Shandong dake birnin Jinan na lardin Shandong dake arewacin kasar Sin.

A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Najib Ahmed ya yi tsokaci kan yanayin karatu a kasar Sin, da yadda ya fahimci ci gaban da wannan kasa take samu a kullum.

Har wa yau, malam Najib ya bada wasu shawarwari ga daliban Najeriya da suke son zuwa kasar Sin don karo ilimi. (Murtala Zhang)