Dole ne Japan ta daina goyon bayan masu ra’ayin nuna karfin soja
2022-08-16 10:34:47 CMG Hausa
Ranar 15 ga watan Agustan bana, aka cika shekaru 77 da kasar Japan ta sanar da mika wuya ba tare da gindaya sharadi ba, amma al’ummomin kasashen duniya suna damuwa matuka, saboda sun ga yunkurin da wasu ‘yan siyasar kasar masu ra’ayin nuna karfin soja suke nunawa, musamman ma kan batun Taiwan.
A kwanakin baya bayan nan, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta sabawa manufar “kasar Sin daya kacal a duniya”, ta kai wa yankin Taiwan na kasar Sin ziyara, inda ta sha suka daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 170. Amma firayin ministan Japan Fumio Kishida ya bayyana yayin da yake ganawa da Pelosy cewa, matakan soja da kasar Sin ta dauka a kusa da tsibirin Taiwan sun kawo kalubale ga tsaron kasar Japan. Ya kara da cewa, Japan da Amurka za su kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan tare.
Hakika Japan ba ta da hakkin yin sharhi kan batun Taiwan ko kadan. Sojojin Japan sun taba kai wa tsibirin Taiwan hari, har da kwace tsibirin da sauran kananan tsibirai a yankin a shekarar 1895, inda Japan din ta yi mulkin mallaka har na tsawon shekaru hamsin, tare kuma da hallaka mazauna yankin Taiwan sama da dubu 600, lamarin da ya jefa Taiwan cikin mawuyacin yanayi mai tsanani.
Kana bayan Japan ta mika wuya a yakin duniya na biyu, kasar Amurka ba ta hukunta masu ra’ayin nuna karfin soja na Japan ba, bisa la’akari da moriyarta, lamarin da ya sa har yanzu masu ra’ayin nuna karfin soja na Japan ke ci gaba da kokarin gudanar da mulkin mallaka a yankin Taiwan.
Kowa ya sani, bai kamata ‘yan siyasar Japan su manta da masifun da suka kawo wa sauran kasashen Asiya makwabtansu ba, ya dace su yi la’akari da darasin tarihi, kuma dole ne su daina goyon bayan masu ra’ayin nuna karfin soja. (Jamila)