logo

HAUSA

Amurka Za Ta Sake dandana Kudar Da Ta Taba Dandanawa A Kabul

2022-08-16 21:34:31 CMG Hausa

Yau shekara guda ke nan da janyewar sojojin kasar Amurka daga Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, bayan da suka shafe shekaru 20 na mamaye kasar, lamarin dake zama alamar gazawar Amurka a Afghanistan. Duk da janyewar Amurka daga Afghanistan, amma ba ta kawo karshen laifuffukan da ta aikata a kasar ba. Ta sanya wa Afghanistan takunkumin tattalin arziki, ta kwace kudaden al’ummar Afghanistan wadanda suke dogara da su sosai. Ta kuma keta ikon mulkin kan Afghanistan yadda take so.

A karshen watan jiya, rundunar sojan Amurka ta kai farmaki ta hanyar amfani da jirgin sama maras matuki a Kabul da sunan “yaki da ta’addanci”, lamarin da ya gamu da suka daga fadin Afghanistan, saboda abin da Amurka ta yi ya saba wa dokokin kasa da kasa, ikon mulkin kan Afghanistan. Amurka ta nuna wa kasashen duniya cewa, za ta ci gaba da tsoma baki a harkokin cikin gidan Afghanistan.

Sai dai, sakamakon tallafin kasa da kasa, ya sa Afghanistan ta jure wahalhalun tsananin sanyi, girgizar kasa, ambaliyar ruwa da takunkumin da aka kakaba mata, ta kuma samu ci gaba wajen kiyaye tsaro da yaki da miyagun kwayoyi.

Bai kamata a manta da jama’ar Afghanistan ba. Kuma kar Amurka wadda ta jefa Afghanistan cikin wahala, ta dora wa wasu laifi, ta bar Afghanistan ba tare da sauke nauyin dake wuyanta ba. Ya zama tilas gwamnatin Amurka ta nemi gafara sakamakon mamaye Afghanistan, ta kuma mayarwa al’ummar Afghanistan kudadensu, ta biya diyyan da ya dace, ta janye takunkumin da ta sanyawa al’ummar Afghanistan cikin hanzari. Kana kuma, kamata ya yi ta koyi darasi daga yakin Afghanistan, ta dakatar da dogaro da karfin soja, da tada kura a wasu kasashe. Idan ta ci gaba da haka, to, za ta sake dandana kudar da ta taba dandana a Kabul. (Tasallah Yuan)