logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijer ya halarci bikin mika alluran rigakafin cutar COVID-19 ga Nijer

2022-08-16 20:29:52 CMG Hausa

A jiya ne, sabon rukunin alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta ba da taimako ga kasar Nijer, suka iso Niamey, babban birnin kasar Nijer, jakadan Sin dake kasar Nijer Jiang Feng, da mukaddashin ministan kiwon lafiya na kasar Nijer wato ministan kula da al’adu da yawon shakatawa da sana’ar hannu na kasar Mohamed Hamid sun halarci bikin mika alluran a filin jiragen sama.

A jawabinsa, jakada Jiang ya bayyana cewa, yayin da ake tinkarar cutar COVID-19, Sin da Nijer suna yin kokari tare. Sin tana son mika alluran rigakafin cutar ga Nijer a matsayin sabon mafari wajen raya tsarin hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin Sin da Nijer har ma da Afirka baki daya.

A nasa bangare, minista Hamid ya bayyana cewa, shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum, ya yaba da kyakkyawar hadin gwiwar dake tsakanin Nijer da Sin. Yana mai cewa, gwamnati da jama’ar Nijar suna godiya ga kasar Sin kan taimakon da take ba ta wajen yaki da cutar COVID-19. Bangaren Nijer zai yiwa al’ummar kasar karin alluran rigakafin cutar don yaki da cutar. Haka kuma Nijer tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin a fannin kiwon lafiya da zurfafa zumunta a tsakaninsu. (Zainab)