logo

HAUSA

Wani hari ta sama ya halaka sama da mayaka 13 na al shabab

2022-08-15 11:18:15 CMG Hausa

Dakarun Somalia da na Amurka sun kashe sama da mayakan al-Shabab 13, ciki har da shugabannin kungiyar, yayin wani luguden wuta ta sama da suka yi a yankin Hiran dake tsakiyar kasar Somalia.

Gidan rediyon rundunar sojin Somalia, ya ruwaito cewa, an kashe mayakan tare da shugabanninsu, haka kuma an lalata maboyarsu yayin luguden wuta da sojojin Amurka suka yi da misalin karfe 2 na yammacin jiya agogon kasar, bisa goyon bayan da suke ba rundunar sojin Somalia wajen yakar ta’addanci a yankin Hiran.

Kawo yanzu dai, rundunar sojin Amurka ba ta tabbatar da rahoton ba. (Fa’iza Mustapha)