logo

HAUSA

Habasha ta kaddamar da yankin ciniki cikin ‘yanci na farko

2022-08-15 10:40:45 CMG Hausa

Firaministan Habasha Abiy Ahmad, ya kaddamar da yankin ciniki cikin ‘yanci na Dire Dawa, wanda shi ne irinsa na farko a kasar, a jiya Lahadi.

Gwamnatin Habasha ta ce yankin na Dire Dawa, zai karfafa tattalin arzikin kasar ta hanyar inganta shige da ficen kayayyaki.

Yankin masana’antu na Dire Dawa da tashar jiragen ruwa ta kan tudu, da tashar jirgin kasa da ta hada Habasha da Djibouti ne suka hade suka zama yankin na ciniki cikin ‘yanci.

Kafa yankunan ciniki cikin ‘yanci, daya ne daga cikin manyan shirye-shiryen habaka tattalin arziki dake cikin shirin raya kasa na shekaru 10 na kasar Habasha. (Fa’iza Mustapha)