logo

HAUSA

Bincike: Daga abubuwa masu nauyi yana ba da kariya daga cutar Alzheimer's disease

2022-08-14 15:21:33 CMG Hausa

 

Wani binciken da masanan kasar Australia suka gudanar ya nuna cewa, daga abubuwa masu nauyi zai iya ba da kariya ga kwakwalwa daga cutar Alzheimer's disease, kamar yadda sakamakon binciken ya nuna. Alzheimer's disease, wani nau’in ciwon karancin basira da dake farawa daga cutar karancin basira, daga bisani ya shafi tunanin mutane da kwarewar magana har ma da gudanar da harkokin yau da kullum.

Masana kimiyya daga jami’ar Sydney (UoS) sun bayyana cewa, samun horon na daukar abubuwa masu nauyi cikin watanni shidda, yana taimakawa wajen rage saurin lalacewar yanayin wasu sassan kwakwalwa wadanda ke da hadarin kamuwa da cutuka, ko kuma dakatar da kamuwa da cutuka a wadannan sassan kwakwalwa.

An gudanar da binciken kan tsoffi 100, wadanda ke da barazanar kamuwa da cutar Alzheimer's disease sakamakon cutar karancin basira da suka riga suka kamu da ita.

Bugu da kari, binciken ya nuna cewa, shan koffi ko ganyen shayi ko kuma dukka biyun, mai yiwuwa ne yana iya rage barazanar kamuwa da shanyewar jiki da cutar karancin basira.

Masu bincike daga jami’ar ilmin likitanci ta Tianjin ta kasar Sin, sun yi nazari kan wasu mahalarta 365,682 daga rumbun adana sumfuran jini da kwayoyin halittar gado na kasar Birtaniya, ‘yan shekaru 50 zuwa 74. Dukkan mahalartan sun bayyana rahoton yadda suke shan kofi da ganyen shayi. A lokacin bin diddigi na shekaru 11.4 da aka fara samun bullar cutuka, wasu 5,079 sun kamu da cutar karancin basira, sannan wasu 10,053 sun kamu da cutar shanyewar jiki a kalla sau daya.

Binciken ya nuna cewa, mutanen dake shan kofuna biyu zuwa uku na koffi, ko kuma kofuna uku zuwa biyar na ganyen shayi a kowace rana, ko kuma suke hadawa duka na kofuna hudu zuwa shida na koffi da ganyen shayi, suna da karancin yiwuwar kamuwa da cutar shanyewar jiki da cutar karancin basira.

Masu nazarin sun kuma duba alakar dake tsakanin nau’ikan koffi da cutar shanyewar jiki da ta karancin basira. Daga ciki nau’ikan garin koffi, da koffin sha yanzu, da wadanda aka fidda sinadarin caffeine daga koffin, an gano masu shan garin koffi sun fi karancin barazanar kamuwa da cutar karancin basira da dai makamantansu.

Koffi yana kunshe da sinadaran antioxidants da bioactive, yayin da ganyen shayi ke dauke da sinadaran caffeine da catechin wadanda ke daidaita yanayin kwakwalwa daga fuskantar wasu matsaloli.(Ahmad)