logo

HAUSA

Mutane 41 sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi a wata majami’a a Gizan kasar Masar

2022-08-14 20:36:14 CMG Hausa

 

Ma'aikatar lafiya ta kasar Masar ta sanar da cewa, a kalla mutane 41 ne suka mutu, kana wasu 12 suka jikkata, biyo bayan wata mummunar gobara da ta tashi a wata majami'ar kibdawa da ke lardin Giza na kasar Masar a jiya Lahadi.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, har yanzu ana kirga gawarwakin mutane da suka mutu, lamarin da ya faru a majami’ar Abu Sifin dake unguwar Imbaba. Tana mai cewa, an aike da motocin daukar marasa lafiya 37 zuwa wurin.

A wata sanarwa ta daban, ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce, gobarar ta tashi ne daga na'urar sanyaya daki da ke hawa na biyu na ginin cocin, sakamakon matsalar wutar lantarki. (Ibrahim)