logo

HAUSA

Sharhi: Afirka wani babban dandalin hadin gwiwar kasa da kasa ne ba fagen takara tsakanin manyan kasashe ba

2022-08-14 18:01:22 CMG Hausa

Kwanan nan, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya kawo karshen ziyararsa a wasu kasashen Afirka guda uku. A yayin ziyararsa a kasar Afirka ta kudu, Mr.Blinken ya gabatar da jawabi dangane da sabbin tsare-tsaren kasar Amurka a kan Afirka, inda ya furta cewa, duk da ja-in-jan da ke kara ta’azzara a tsakanin Amurka da sauran manyan kasashen irinsu Sin da Rasha, Amurka dai ba za ta bukaci kasashen Afirka su zabi wani matsayin da za su dauka ba. Duk da haka, Blinken ya yi ta furta “barazanar” da Sin da Rasha ke haifarwa a kalamansa.

Sai dai tuni bangarori daban daban a kasashen Afirka sun gane ainihin abin da Mr. Blinken ke neman cimmawa. Don haka, a yayin da take ganawa da manema labarai tare da Mr.Blinken, ministar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu Naledi Pandor ta jaddada cewa, kasashen Afirka suna da ‘yancin kulla da kuma bunkasa hulda da mabambantan kasashe. Kafofin yada labarai da masana na Afirka ma sun soki sabbin tsare-tsaren kasar Amurka a kan Afirka, ganin yadda take yin amfani da kasashen Afirka wajen yin takara da manyan kasashe, a maimakon kawo wata moriya ga kasashen Afirka. Sun kuma yi nuni da cewa, “sabon cacar baka” wani tarko ne da kafofin yada labarai na kasashen yamma suke yunkurin danawa, amma kasashen Afirka ba sa so su zabi wani matsayin da za su dauka ba.

A hakika, kasashen duniya na zaman cude-ni-in-cude-ka ne, kuma makomarsu daya ce. Sai dai abin bakin ciki shi ne, Amurka wadda ra’ayin babakere da nuna fin karfi ya zame mata jiki, ta fi karkata ne kawai ga takara a wannan duniya, a maimakon hadin gwiwar cin moriyar juna. Sabo da haka, Amurka ta kasa fahimtar irin zumunta da hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Afirka, kasancewarsu kasashe masu tasowa ne duka, baya ga manufar makomar bai daya ga dukkanin ‘yan Adam da kasar Sin ta gabatar.

A yayin ziyararsa Nijeriya a farkon shekarar bara, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi nuni da cewa, Afirka wani babban dandalin hadin gwiwar kasa da kasa ne ba fagen takara tsakanin manyan kasashe ba. Alkawari ne da kasar Sin ta dauka, kuma kasar ta cika.

Duk da zancen “barazanar kasar Sin” da Amurka ke kokarin yayatawa, ba za a iya kawar da kai daga nasarorin da kasashen Sin da Afirka suka cimma a hadin gwiwarsu ba. Hanyoyin jirgin kasa, da titunan mota, da tashoshin jiragen ruwa, da manyan gine-ginen da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa a Afirka, duk suna nan a zahiri, wadanda kuma suke amfanar al’ummun kasashen a zahiri. Kasashen Afirka ba sa bukatar aminiya wadda za ta rika jirkita gaskiya, kuma idanun ‘yan Afirka a bude suke. In dai da gaske Amurka tana son taimakawa nahiyar Afirka, ya dace ta dauki matakan zahiri, maimakon ta yi amfani da manyan tsare-tsarenta kan nahiyar Afirka, don hana ci gaban hadin-gwiwar Afirka da wasu kasashe. (Mustapha Bulama)