Yu Yanqia: Ina amfani da ilimin da na koya don ba da gudummawa ga ci gaban garinmu
2022-08-15 19:58:20 CRI
A watan Yunin wannan shekara, Yu Yanqia, mai shekaru 23 da haihuwa, kuma 'yar asalin kabilar Lisu, ta yi nasarar kammala karatunta a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Biyu, ta Jami'ar Kiwon Lafiya ta Kunming. Ta kuma yanke shawarar komawa garinsu dake yankin Nujiang don yin aiki, kuma ta zama ma'aikaciyar lafiya a asibitin jama’ar yankin Nujiang.
Gidan su Yu Yanqia yana kauyen Bula, na garin Maji, dake yankin Nujiang na lardin Yunnan a kudu maso yammacin kasar Sin.
A shekarar 2007, kamar yawancin mutanen da ke gabobi biyu na kogin Nujiang, mazauna kauyen Bula, sun dogara da hawa igiya don tsallake kogin, ciki har da Yu Yanqia, wadda ke bukatar hawa igiya wajen tafi makarantar dake tsallaken kogin.
Wata rana, Yu Yanqia sanye da riga mai ruwan hoda, kuma dauke da jakar makaranta, ita kadai tana hawa igiya domin zuwa makarantar firamare ta Bula da ke daya gefen kogin Nujiang, wasu ‘yan jarida dake ziyara a wurin sun dauki hotonta.
A wancan lokaci, Yu Yanqia tana yar shekara 8 kacal, kuma ta shiga aji daya na firamare. Dole ne ta haye kogin ta hanyar hawa igiya sau biyu a ko wace rana, kuma ta shafe shekaru biyu tana haye kogin a kan igiya ita kadai.
Har zuwa yanzu, Yu Yanqia tana iya tunawa da yadda take ji a yayin da take hawan igiya, ta ce, “Karar iskar tana busawa a kunnuwana, da rurin kogin da ke kasa da ni, da bugun zuciyata mai tsanani”.
A wancan lokacin, ganin yadda Yu Yanqia ke hawan igiya ita kadai don ratsa kogin a kowace rana, 'yan jaridun da ke wurin sun yi matukar kaduwa, sannan suka hada kan kafofin yada labarai da dama a fadin kasar Sin, domin tara kudade daga al'umma, sannan aka gina wata gadar soyayya a bakin kogin a gaban makarantar firamare ta Bula.
A watan Maris na shekarar 2008, aka kammala gadar soyayya, kuma masu ba da rahoto a kan kafofin watsa labaru, da masu kulawa sun baiwa Yu Yanqia damar haye gadar a karon farko ta kan gadar.
Yu Yanqia, wacce ta ga gadar a karon farko a rayuwarta, bayan ta yi tattaki zuwa tsakiyar gadar, ta kalli ruwan kogin Nujiang da ke karkashin gadar, ta daina tafiya saboda tsoro. A karshe dai, a karkashin taimakon ma'aikatan da ke wurin, ta wuce kogin.
Makomar Yu Yanqia ta canja tun daga wancan lokacin.
Bayan kammala gina gadar soyayya, a karkashin taimakon mutane masu kulawa, Yu Yanqia ta samu damar ziyartar biranen Kunming, da Beijing da sauran wurare, kuma a karon farko ta ga duniya mai ban sha'awa, ban da yankin kogin Nujiang.
Bayan samun sabon fata na rayuwa, Yu Yanqia tana da karfi sosai, na kafa makomar gaba mai kyau. Ta ce, "Kamar akwai karin haske a kan hanya ta mai duhu, kuma kamar wahalar da nake sha kan rayuwa ta ta ragu, don haka na karfafa yin kokari kan karatu."
A shekarar 2018, Yu Yanqia ta shiga Kwalejin Kiwon Lafiyar ta Biyu ta Jami'ar Kiwon Lafiya ta Kunming da maki 568, inda ta zama yarinya ta farko a kauyen su da ta samu shiga jami'a.
A yayin da Yu Yanqia ke kokarin karatunta, a sa’i daya kuma, kawar da fatara, da farfado da karkara na ci gaba da gudana a sassa biyu na kogin Nujiang.
Sakamakon tallafin kudin da aka samu bisa manufofin kasar Sin, dangin Yu Yanqia sun kaura daga gefen dutse zuwa bakin kogi, kuma sun gina sabon gida. Ita ma na iya kara yin karatu sakamakon tallafin kudi bisa manufa. Kana kuma, igiyar da aka yi amfani da su don tsallaka kogin a cikin kwazazzabin Nujiang, duk an maye gurbinsu da ingantattun gadoji da aka gina da karfe da kankare a shekarar 2016, wanda ya sa aka samar da sauki ga jama’ar kabilu daban daban a fannin tafiye-tafiye. Baya ga haka, an gina wata babbar gada a gefen kogin da ke kusa da gidan su Yu Yanqia.
Kyakkyawar hanyar mota da aka gina bisa kogin Nujiang ta soma aiki, an kuma gaggauta raya sana’ar yawon shakatawa a gabobin kogin, da dai sauran ayyukan da aka yi don bunkasa yankin, duk sun sanya yanayin yankin kogin Nujiang da aka rufe a baya ya soma canzawa.
Canjin makomarta, da kuma ci gaban garinsu cikin sauri, ya samo asali ne daga kulawa da taimakon kasar, da ma bangarori daban daban na al’umma, wanda Yu Yanqia ta yi tunani da su a zuciyarta. Tun shigarta jami'a, ta kuduri aniyar bautawa garinsu bayan ta kammala karatu. Ta ce, "A da, na sadu da mutane da yawa da suka ' kunna min fitulu', in ba don taimakonsu ba, da ban kasance yadda nake a yanzu ba. Ina matukar godiya a gare su."
A jajibirin kammala karatunta a jami’a, Yu Yanqia, ta bayyana sha'awarta ta komawa Nujiang ga malamanta. Ta dade tana jiran asibitin garinsu domin daukar jarabawar, kuma ba ta taba tunanin samun aikin yi a sauran wurare ba, don haka ta rasa damar samun aikin yi da yawa.
Irin ra’ayin na Yu Yanqia, na bautawa garinta ya burge malamanta sosai. Daga baya, lokacin da shugabannin makarantar suka je yankin Nujiang don gudanar da aikin inganta samar da ayyukan yi, sun kawo takaitaccen tarihin neman aikin yi na Yu Yanqia na musamman, don ba da shawara ga masu daukar ma'aikata. A karshe, asibitin jama’ar Nujiang ya karbi Yu Yanqia.
Yu Yanqia, wadda za ta fara aiki a watan Satumba mai zuwa, tana sa ran kyautata makomarta a nan gaba. Ta ce,“A nan gaba, ba zan yi kasa a gwiwa ba, wajen nuna kwarewar makarantarmu yayin da nake aiki, kuma zan yi kokarin yin amfani da ilimin da na koya, wajen bayar da gudummawa ga bunkasuwar harkar lafiya a garinmu.”