logo

HAUSA

The Guardian: Kalaman fatar baka kadai ba za su gamsar da kasashen Afirka ba

2022-08-13 17:06:52 CMG Hausa

Jaridar “The Guardian” da ake wallafawa a Burtaniya, ta fitar da wani sharhi dake cewa, kalaman fatar baka daga tsagin mahukuntan Amurka kadai, ba za su gamsar da kasashen Afirka, har su sauya matsayin kawancen su ba.

Jaridar na wannan tsokaci ne, bayan da sakataren wajen Amurka Antony Blinken ya kammala ziyarar wasu kasashen Afirka 3, a ziyara ta 2 da ya kai nahiyar, tun bayan kama aiki a gwamnatin shugaba Joe Biden.

Yayin wannan ziyara ta 2, wadda aka tsara za ta baiwa Amurka zarafin sake gina kawancen Amurka da kasashen Afirka, Blinken ya saukar da kai, ya kaucewa yiwa Afirka kallon kaskanci, irin wanda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya rika yi, ko zamewa kasashen na Afirka mai ba da darasi, kan bukatun su, da abubuwan da suka fi dacewa su zaba.

Jaridar ta ce duk da dai Blinken ya dage cewa, burin Amurka na karfafa alaka da Afirka, ba ya nufin fitar da wata kasa daga kawancen Afirka, a hannu guda, ziyarar ba ta rasa nasaba da damuwar da Washington ke nunawa, game da karin karbuwar kasar Sin a nahiyar, da ma ziyarar da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya kai wasu kasashen na Afirka 4 a watan da ya gabata, domin neman goyon baya, da kara karfafa dangantaka da sassan nahiyar.

Mafi yawan tallafin Amurka ga kasashen Afirka ba ya wuce fatar baki, musamman idan aka waiwayi batun yadda Amurkan ta boye tarin alluran rigakafin COVID-19, lamarin da ya jefa nahiyar Afirka cikin yanayin na kamfar rigakafin, baya ga batun gazawa wajen aiwatar da sahihan matakan shawo kan sauyin yanayi, da kare dazuka masu tarin tsirrai.  (Saminu Alhassan)