logo

HAUSA

Jirgin ruwan farko na hatsin Ukraine da zai nufi Afirka ya isa tashar ruwa

2022-08-13 17:02:00 CMG Hausa

A jiya Juma’a ne jirgin ruwan farko na dakon hatsin kasar Ukraine, wanda zai nufi nahiyar Afirka ya isa tashar ruwan Pivdennyi, tun bayan da rikicin kasar da Rasha ya barke a watan Fabarairu.

Ministan samar da ababen more rayuwa na Ukraine Oleksandr Kubrakov, shi ne ya bayyana hakan cikin wani sakon Tiwita, yana mai cewa, nan ba da jimawa ba, hatsi daga kasar Ukraine zai isa kasar Habasha.

A wani ci gaban kuma, a jiya dai, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya nada Amir Mahmoud Abdulla daga kasar Sudan, a matsayin shugaban tsare tsare, na tabbatar da nasarar shigar da hatsi sassan duniya ta bahar Aswad. (Saminu Alhassan)