logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin dake Nijar ya gana da tsohon shugaban kasar

2022-08-13 20:40:36 CMG Hausa

Jiya Jumma’a, jakadan kasar Sin a Nijar Jiang Feng, ya gana da tsohon shugaban janhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi mai zurfi, kan dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu. Guo Xueli, mai ba da shawara kan harkokin siyasa na ofishin jakadancin Sin dake Nijar, ya halarci taron.

Jiang ya yi tsokaci, game da gudummawar da Issoufou ya bayar, wajen sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Nijar, da sada zumunci tsakanin al'ummomin kasashen biyu. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na son yin hadin gwiwa da Nijar, wajen daga dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangaren, Issoufou ya ce, kasar Sin na daya daga cikin muhimman abokan hadin gwiwar Nijar. Yana kuma fatan ci gaba da yin kokari, wajen sada zumunta tsakanin Nijar da Sin, da kuma sa kaimi ga samun karin nasarori a fannin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)