logo

HAUSA

Sin na amfani da hanyoyin motsa jiki wajen gina kyakkyawar makomar al’umma

2022-08-12 15:44:55 CRI

Idan mutum na kewaya sassan kasar Sin cikin shekarar bana, akwai yiwuwar ya gamu da gungun mahaya kekuna suna tafe cikin sauri.

Hawa keke, ya zama wata hanya ta sufuri ga kaso mai yawa na magidanta Sinawa, amma a baya bayan nan, hawa keke ya dauki sabon salo, inda Sinawa da dama, suka rungumi hawa keke a matsayin hanyar motsa jiki da wasannin samun nishadi, bisa sauyin yanayin rayuwar birane da kuma al’adu.

Karuwar mahaya keke, ya haifar da fadadar kasuwar kekuna. Hakan ya sa a wasu lokuta kekune masu karko, da kayan gyaran su ke karewa a shaguna, hakan ya kan sa masu sayayya da yawa kan yi jira kafin samun irin kekunan da suke bukata.

A daya hannun, manhajar kekunan hawa na haya domin al’umma, irin su “Meituan Bike” sun samu karbuwa matuka da gaske a biranen Beijing, da Shanghai da Shenzhen. Kuma alkaluman kididdiga na nuna karuwar karbuwar su a ragowar sassan kasar Sin baki daya.

Baya ga wannan, akwai wasan jefa faranti, wanda Amurkawa dake aiki a kasar Sin suka shigo da shi kusan shekaru sama da 30 da suka gabata, da wasan zamiyar allo mai tayoyi, wadanda a yanzu al’ummar Sinawa ke nishadantuwa da su, kuma suke kara samun karbuwa.

Ana iya cewa, bunkasar karin wasannin motsa jiki a kasar Sin, na da nasaba da bullar annoba, da karin kula da mutane ke nunawa ga kare muhalli, da fannonin kiwon lafiya, dukkanin wadannan suna kara ingiza kaunar da Sinawa ke da ita game da wasannin motsa jiki masu karfafa gangar jiki, da kuma lafiyar tunani a wannan duniya dake cike da rashin tabbas. 

Ranar Litinin din farkon makon nan, ake cika shekaru 14 a fara bikin ranar motsa jiki ta kasar Sin, kuma tun daga shekarar 2009, wannan rana ke ta kara samun karbuwa a jadawalin abubuwan da suka shafi motsa jiki tsakanin Sinawa. 

Da fari an kebe ranar ne domin ta zamo yinin nuna muhimmancin motsa jiki, tare da kira ga Sinawa da su shiga harkokin motsa jiki yadda ya kamata. Daga nan ne kuma ranar ta kara fadada, tare da ingiza bude karin cibiyoyin motsa jiki, inda a yayin bikin ranar, wasu cibiyoyin motsa jiki da wuraren shakatawa dake sassan kasar Sin, ke bayar da damar shiga ayyuka da suke shiryawa a matsayin bangare, na gangamin wayar da kai na kasa, domin yayata salon rayuwa mai cike da koshin lafiya.

Domin karfafa gwiwar mutane su shiga karin harkokin motsa jiki, gwamnatin kasar Sin ta fitar da tsarin gudanarwa a shekarar bara, da nufin sanya kaso 38.5 bisa dari na daukacin al’ummun kasar shiga harkokin motsa jiki akai akai nan da shekarar 2025. 

Shirin wanda za a aiwatar tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, yana kunshe da manufofi 8, wadanda suka hada da kara azamar samar da wuraren motsa jiki da wasanni, da tsara gudanar da wasanni na al’umma, da shirya gasanni, da kuma ingiza ci gaban masana’antun wasanni masu inganci da dai sauran su.

Bisa tsarin shigar da mutane tun daga matakin farko na al’umma cikin harkokin raya wasanni, birnin Shanghai shi kadai, zai shirya harkokin wasanni ta yanar gizo da kuma a zahiri har 242, tsakanin ranakun 6 zuwa 14 ga watan nan na Agusta, kuma za a bude wuraren gudanar da wadannan harkokin wasanni har 400, domin jin dadin jama’a.

Kwazon kasar Sin na yayata muhimmancin wasannin motsa jiki, ya fara haifar da kyakkyawan sakamako. Wani rahoton baya bayan nan da aka fitar a bana, ya nuna yadda adadin Sinawa da shekarun haihuwar su ya haura 7, ke kara shiga harkokin wasanni a kalla sau daya a mako, adadin da ya kai kaso 67.5 bisa dari na al’ummar kasar, wanda ya nuna karuwar kaso 18.5 bisa dari, sama da wanda aka samu a shekarar 2014.

Nasarar da aka samu wajen kara yayata muhimmancin wasannin motsa jiki, na kuma da nasaba da nasarar kammala gasar Olympic ta birnin Beijing, da ajin gasar bangaren masu bukatar musamman ko “Paralympic” ta lokacin hunturu da ta gabata a kasar Sin.

Yayin da aka yi nasarar cimma burin shigar ‘yan kasar da yawan su ya kai miliyan 300 cikin harkokin wasannin lokacin hunturu, Sin ta shirya tsarin da zai tabbatar ana ci gaba da amfani da kayayyakin da aka tanada domin gasar Olympic din da ta shude yadda ya kamata.

Dukkanin wuraren wasannin kankara na gasar Beijing 2022, masu kunshe da salon kirkire-kirkire, da fasahar amfani da iskar “carbon dioxide” domin samar da sanyi, an tsara ci gaba da amfani da su domin wasannin kankara, da wasannin linkaya, da sauran wasanni daban daban cikin shekaru masu zuwa. 

Hakan wani bangare ne, na faffadan burin mayar da wadannan wurare, cibiyoyin gudanar da wasanni da za a iya amfani da su a duk tsawon shekara, kana wurare da za su samar da cikakken alfanu, a fannin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar dake kewaye da su.

Ko shakka ba bu, Sin ta tabbatar da manufar hade shirya gasanni da hidimtawa al’umma. Kuma ranar motsa jiki ta kasa, ta wakilci abubuwa da dama, baya ga tunawa da muhimmancin motsa jiki, ta kuma zamo wata dama ta dora kasar Sin kan turba ta cimma nasarori masu yawa a nan gaba.