logo

HAUSA

Masanan Afirka Da Sin: Kasashe Masu Tasowa Suna Kokarin Tabbatar Da Tsarin Duniya Mai Yakini

2022-08-12 14:39:00 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, aka gudanar da taro na 11 na dandalin masanan kasashen Afirka da Sin CATTF, a birnin Beijing na kasar Sin, inda dimbin masana da jami’ai daga bangarorin Afirka da Sin suka halarci taron, tare da tattauna batun raya huldar dake tsakanin Afirka da Sin, da aiwatar da shirin tabbatar da ci gaban duniya. A ganin mahalarta taron, kasashen Afirka da kasar Sin, da sauran kasashe masu tasowa, za su iya taka muhimmiyar rawa a kokarin tabbatar da tsarin duniya a wannan zamanin da muke ciki. (Bello Wang)