logo

HAUSA

Amurka: “Moriyata ta fi gaskiya”

2022-08-12 16:20:00 CMG HAUSA

Kasar Sin ta mayar da martani game da ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan. Amma, wasu ‘yan siyasar Amurka suna ganin matakai masu dacewa da Sin ta dauka a matsayin wadanda suka tsananta halin da ake ciki a yankin. Yau “duniya a zanen MINA” na bayyana yadda kasar Amurka ke nuna girman kai a duniya.

A hakika, kasar Sin ta sha bayyana adawarta da ziyarar Pelosi a yankin Taiwan ta hanyoyi daban-daban a matakai daban-daban. Kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya bayyana cewa, Amurka ta nace ga kin yarda da balle yankin Taiwan daga kasar Sin, amma ba da dadewa ba, ya manta da wannan batu, har ya zuga Pelosi da ta kai ziyara a yankin Taiwan. Ganin yadda halin da ake ciki a yankin ya kara tsananta, sai suka dora laifi kan kasar Sin. Shin ba su san gaskiyar al’amarin game da yankin ba? A’a, suna sane sosai, amma a ganinsu, moriyarsu ta fi gaskiya.

A yau 10 ga wata, Sin ta gabatar da takardar bayani dangane da batun Taiwan da dinkuwar kasar Sin a sabon zamani, don ja kunnen mahukuntan yankin Taiwan da ma wasu ‘yan siyasar Amurka: dole ne su mutunta ikon mulkin kasar Sin, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar, kuma su mutunta gaskiya da yin watsi da girman kai. (Mai zane: MINA)