logo

HAUSA

Yunkurin Amurka kan sana’ar kera sassan na’urorin laturoni ba zai yi nasara ba

2022-08-12 10:52:45 CMG Hausa

Kafofin watsa labaru na kasar Amurka ba su nuna kyakkyawar makoma ga dokar dake da alaka da sassan na’urorin laturoni da sauran ayyukan kimiyya da shugaban kasar Joseph Biden ya sanyawa hannu ba. Jaridar The New York Times ta bayyana cewa, dokar ta bayyana yunkurin kasar, amma watakila amfaninta ba mai dogon zango ba ne.

Me ya sa ake nuna shakku kan dokar mai kunshe da shafuna fiye da dubu daya? Domin ta shaida yunkurin kasar Amurka ta tsara wani shirin dake da nasaba da sana’ar kera sassan na’urorin laturoni da sauran ayyukan kimiyya da darajarsu ta kai kimanin dala biliyan 280, don jan kamfanoni su kafa rassa a kasar, da sa kaimi ga tattara kamfanonin kera sassan na’urorin laturori na zamani a kasar, lamarin da zai sanya Amurkar kan gaba a fannin kimiyya da fasaha a duniya.

Bisa kididdigar da aka yi, jimilar sana’o’in da suka shafi kera na’urorin da ba sa karbar lantarki a kasar Amurka a shekarar 1990, ya kai kashi 37 cikin dari bisa na duniya, amma yawansu ya ragu zuwa kashi 12 cikin dari a shekarar 2020, saboda sana’o’in sun fita zuwa sauran kasashen duniya. A don haka, Amurka ke kokarin mayar da su kasarta.

A shekarun baya-baya nan, wasu kasashen duniya ciki har da kasar Sin, sun samu gagarumin ci gaba kan sana’ar kera na’urorin da ba sa karbar lantarki, lamarin ya haifar da damuwa ga Amurka. Don haka kasar ta gabatar da dokar don tilastawa kamfanonin da abin ya shafa, zabar amincewa da kudurinta ko a’a, don kawo cikas ga wadannan kasashe ciki har da kasar Sin, da tabbatar da matsayin Amurka na kan gaba a wannan fanni. Wannan, shi ne dalilin da ya sa Amurka ta gabatar da irin wannan doka.

Kasar Amurka tana da ‘yancin raya kanta, amma bai kamata ta kawo cikas ga ci gaban sauran kasashe ba. Yunkurinta na kare sana’ar kera na’urorin laturori ba zai yi nasara ba.(Zainab Zhang)