logo

HAUSA

Dakarun Nijeriya sun kashe ’yan ta’adda 29 tare da cafke wasu 55 a arewa maso gabashin kasar

2022-08-12 11:13:58 CMG HAUSA

 

Rundunar sojin Nijeriya ta ce, dakarunta sun kashe akalla ’yan ta’adda 29 tare da cafke wasu 55, yayin wani samame da suka kai yankin arewa maso gabashin kasar, cikin makonni biyu da suka gabata.

Kakakin rundunar Bernard Onyeuko ya shaidawa wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, an kuma ceto mutane 52 da ’yan ta’addan suka sace a yankin.

Ya kara da cewa, a wannan lokaci, jimilar mayakan BH 1,755 da iyalansu ne suka mika wuya ga dakarun gwamnati, wadanda ke ci gaba da farautar mayakan a kauyuka da tsaunika da garuruwa da biranen dake yankin arewa masu gabashin kasar.

A cewar kakakin, an adana dukkan bayanan mutanen da suka mika wuya da iyalansu, sannan an mika su ga hukumomi masu ruwa da tsaki.

Har ila yau, Bernard Onyeuko ya ce, sojoji sun kuma kashe babban kwamandan kungiyar ISWAP, wato Alhaji Modu, wanda aka fi sani da Bem Bem tare da mayakansa a ranar 3 ga watan, yayin wani hari ta sama da suka kai kauyen Degbawa dake kusa da tsaunikan Mandara na yankin karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno. (Fa’iza Mustapha)