logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Najeriya ya gana da ministan yankin Abuja da ministan zirga-zirga

2022-08-12 11:23:03 CMG HAUSA

 

Jakadan Sin dake Najeriya Cui Jianchun ya gana da ministan yankin Abuja Muhammadu Bello da sabon ministan sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, inda suka tattauna game da hadin gwiwar kasashen biyu.

Taron wanda ya gudana a jiya, ya kuma samu halartar shugaban kamfanin CCECC mai ayyukan gine-gine, dake ziyara a kasar, Liu Weimin.

Yayin ganawa tsakankin Cui Jianchun da Muhammadu Bello, sun waiwayi ci gaban da bangarorin biyu suka samu na hadin kai a yankin hedkwatar kasar da ayyukan da suka ciyar da habakar tattalin arziki da samar da ilmi. Kuma bangarorin biyu sun kai ga matsaya cewa, za su kara hadin kai a nan gaba, don fidda sabbin hanyoyin zuba jari da hadin gwiwa da ma ingiza aikin shuka laimar kwado na ba da misali.

Ban da wannan kuma, yayin da Cui Jianchun ya gana da minista Mu’azu Jaji Sambo, sun waiwayi hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin layin dogo, har ma sun kai ga matsaya daya cewa, Najeriya mai fadin filaye na da boyayyen karfi a fannin tattalin arziki, kuma bangarorin biyu za su dukufa kan aikin kyautata yanayin tsarin layukan dogo a fadin kasar, musamman ma layin dake tsakanin Kaduda da Kano, inda za a yi kokarin ganin an fara amfani da shi a rabin farkon shekarar badi. (Amina Xu)