Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan
2022-08-12 16:45:32 CMG Hausa
Hausawa dai na cewa: "komai nisan jifa, kasa za ta dawo". A nan ina ma nuni da batun Taiwan a kan cewa ko ba dade, ko ba jima, Taiwan za ta dunkule ko kuma za ta hade da jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kasancewar Taiwan wani yanki ne karkashin kasar ta Sin.
A kwanan nan ne ofishin kula da harkokin Taiwan da na watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin a Beijing suka fitar da wata takardar bayani kakkarfa mai taken "batun Taiwan da dunkulewar kasar Sin a sabon zamani". Takardar dai tana kunshe da gargadi da jan kunne ga tsirarrun ’yan aware na tsibirin Taiwan tare da masu ingiza su daga kasashen ketare musamman ma kasar Amurka.
Idan ba a manta ba a wani kokarin tada zaune tsaye da Amurka ta yi a kwanan baya a yayin da kakakin majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi ta kai ziyara tsibirin Taiwan duk da gargadin da kasar Sin ta yi, ya kawo cece kuce da gurbata dangantaka tsakanin kasashen biyu. A sakamakon wannan tada husuma ne ma sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin (PLA) suka yi wani abun da ya nuna taunar tsakuwa domin aya ta ji tsoro a yankin tsibirin na Taiwan da kewaye domin mika sako cewa kasar Sin fa ba za ta yarda da wata rashin kunya da cin mutunci a yankin da ke mallakarta ba.
Kamar yadda na saba ambatar matsayina a kan batun Taiwan, ina nanata rashin gamsuwata ga yadda wasu kasashen ketare musamman Amurka take tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, har ma a ce a kan batun Taiwan wanda ita kanta kasar Amurka ta tabbatar da yankin na Taiwan yanki ne na kasar Sin, kuma kasar Sin daya ce tak a duniya. Kasar Amurkan dai ta rattaba hannu a shekarar 1978 a kan wannan batu. Bugu da kari, akwai wani kuduri mai lamba 2758 wanda aka zartas a babban zauren majalisar dinkin duniya MDD da ya tanadi manufar kasar Sin daya ce a duniya, wanda daukacin kasashen duniya sun yi ammana da shi.
Ina mai matukar jinjina ma kasar Sin da ta bugi gaba ta wallafa wannan takardar bayanin da ta nuna cewa ita fa ba kanwar lasa ba ce, kuma tana nan a kan bakanta na ganin cewa Taiwan ta dawo ta dunkule da mahaifarta a tafarkin "kasa daya, tsarin mulki biyu". Kamar yadda na ambata da farko, sanin kowa ne cewa tun asali Taiwan yanki ne a karkashin kasar Sin kuma mallakarta ne, wannan batu dai yana da ingantaccen tushe na tarihi da doka. A wasu bayanai da takardar da aka watsa suka kunsa, sun nuna cewa manufar kasar Sin daya tak, na wakiltar duk matsayar kasa da kasa, kuma ta yi daidai da ka’idojin huldar kasa da kasa.
A karshe ina son jawo hankalin tsirarrun ’yan aware na Taiwan da kasashe masu zuga su da su yi hattara kuma su lura da take taken su wanda suke nuna neman tashin hankali karara a tsibirin na Taiwan. Jama’ar Taiwan kamar yadda tarihi ya nuna Sinawa ne, ba ja in ja a nan ya kamata su yi la’akari da cewa babu wanda zai fi son su idan ba ’yan uwansu Sinawa ba, kuma abun da ya fi masu alheri shi ne dunkulewa da hadewa da ainihin jamhuriyar jama’ar kasar Sin domin ci gaba da samun zaman lafiya.
Babban kuskure ne idan Taiwan da ’yan awarenta suka ci gaba da bayar da kansu ga ’yan kasar waje masu neman fitina. Wannan ba abin da zai tsinana masu sai rikicin da ba wanda ya san yanda zai kare. (Lawal Sale)