logo

HAUSA

Tarihi baya mantuwa

2022-08-11 15:55:33 CMG Hausa

Tun bayan fara cece-kuce game da haramtacciyar ziyarar da kakakin majalissar dokokin kasar Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na kasar Sin, masharhanta da dama ke ta bayyana mahangar su, don gane da burin Amurka na haifar da baraka ga kasar Sin, da lalata yanayin zaman lafiya da tsaro a zirin Taiwan.

To sai dai kuma, ga dukkanin alamu Amurka ba za ta yi nasara ba a wannan mummunar manufa, ganin cewa tuni mahukuntan Sin din suka tsara dukkanin manufofi, na dinkuwar daukacin sassan kasar cikin lumana, ciki har da yankin na Taiwan. Wannan manufa ce da daukacin al’ummar Sinawa ke marawa baya, wadda kuma ta yi daidai da manufar farfadowar kasar Sin a sabon zamani.

Batun dinkuwar yankin Taiwan da sauran sassan kasar Sin, na da alaka da burin daukacin Sinawa tun fil azal, kuma ya dace da manufofin JKS, da gwamnatin kasar Sin. Dukkanin wadannan sassan suna nacewa manufar wanzar da zaman lafiya, da daidaito a zirin Taiwan, suna kuma daukar matakai na ingiza manufar dunkulewar yankunan kasar Sin bisa doka.

A hannu guda kuma, Amurka da wasu sassan ’yan siyasar kasashen yamma na ta yunkurin haifar da baraka, ta amfani da batun yankin Taiwan, musamman a shekarun baya bayan.

Kamar yadda tarihi ba zai manta da yadda Amurka ta haifar da tashe tashen hankula da yake-yake a sassan kasashen duniya daban daban ba, haka ma tarihi ba zai manta da mugun nufin Amurka na amfani da yankin Taiwan wajen haifarwa kasar Sin baraka ba. Bahaushe dai kan ce “Idan za ka gina ramin mugunta to ka gina shi gajere”. Domin wata kila, wanda ya gina ramin shi ne zai auka a cikinsa.

Lokaci ya yi da Amurka, da masu mara mata baya a wannan mummunar aniya, za su yi karatun ta nutsu, su san cewa, duk wani yunkuri na kawowa kasar Sin baraka ba zai taba yin nasara ba! (Saminu Hassan)