logo

HAUSA

Guterres ya taya murnar kada kuri’a a zaben Kenya cikin lumana

2022-08-11 13:50:01 CMG HAUSA

 

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya taya al'ummar kasar Kenya murnar kada kuri'a cikin lumana, a babban zaben kasar da aka gudanar ranar Talata.

Guterres ya yi imanin cewa, dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa gami da al'ummar Kenya, za su ci gaba da kwantar da hankula, da yin hakuri da mutunta tsarin zaben, yayin da suke jiran bayyana sakamakon zaben kamar yadda doka ta tanada.

Sanarwar ta bayyana cewa, "babban jami’in na MDD, ya nanata kudirin majalisar na ci gaba da ba da goyon baya ga kokarin hukumomin Kenya da al'ummar kasar, wajen ciyar da tsarin demokuradiyya a Kenya gaba."

A ranar Talata ce, 'yan kasar Kenya suka kada kuri'unsu, domin zaben shugaban kasa na biyar, da 'yan majalisar dokokin kasar, da na majalisar dattawa, da kuma gwamnonin kananan hukumomi.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kenya, ya fada a yammacin ranar Talata cewa, an kammala kada kuri'a a babban zaben kasar a dukkan runfunan zabe, har ma an fara kidaya kuri'un. (Ibrahim Yaya)