logo

HAUSA

Kamaru za ta hada gwiwa da Najeriya don bunkasa noman Ayaba da plantain

2022-08-11 10:49:12 CMG HAUSA

 

Manoman Ayaba da Plantain a kasashen Kamaru da Najeriya sun amince su hada kai don bunkasa noman amfanin gona a kasar.

An cimma yarjejeniyar ce ranar Talata a Yaounde, babban birnin kasar Kamaru, bayan da masu samar da kayayyakin suka gana da ministan noma da raya karkara na kasar, Gabriel Mbairobe.

Jagoran tawagar Najeriya a tattaunawar, Albert Agha Ngwana ya bayyana cewa, Najeriya kasa ce mai karfin tattalin arziki da yawan al’umma a Afirka, yayin da kasar Kamaru ke zama babbar kasar noma, wadda za ta iya ciyar da wannan al'umma. Don haka, kasashen biyu za su iya gyara tattalin arzikinsu da ma kara samar da ayyukan yi.

Wakilin wata kungiyar hadin gwiwar aikin gona da gandun daji, wanda ya tarbi tawagar Najeriya a kasar Kamaru Samuel Tony Obam Bikoue ya bayyana cewa, Ayaba shi ne amfanin gona na uku da kasar Kamarun take fitarwa zuwa ketare, bayan mai da katako, amma kasar na kokarin ganin ya zama amfanin gona na farko da take fitarwa zuwa kasashen waje nan da shekarar 2025. (Ibrahim Yaya)