logo

HAUSA

Saliyo ta kafa dokar hana fita a fadin kasar bayan wata zanga-zangar da aka yi a kasar

2022-08-11 14:24:34 CMG HAUSA

 

Jiya ne, kasar Saliyo ta kafa dokar hana fita a fadin kasar, bayan wata zanga-zangar da aka yi a wasu wuraren kasar wadda ke yammacin Afirka.

Mataimakin shugaban kasar Mohamed Juldeh Jalloh ne ya sanar da dokar ta kafar talabijin. Yana mai cewa, an dauki matakin ne don yayyafa ruwa a lamarin tare da dawo da kwanciyar hankali a cikin kasar.

A jiya ne, dubban masu zanga-zanga suka bazama kan titunan Freetown, babban birnin kasar da wasu sassan kasar. Sun yi kira ga gwamnati da ta warware matsalolin tattalin arzikin da tsadar rayuwa da ’yan kasar ke fuskanta.

A halin da ake ciki, zanga-zangar ta kawo cikas ga harkokin kasuwanci, inda shaguna a rufe suke a fadin babban birnin kasar, saboda fargabar masu zanga-zangar za su iya kai musu hari.

Gwamnati ta bukaci sojoji da su taimakawa 'yan sanda su yi aiki tare wajen shawo kan zanga-zangar da ake yi cikin kasar. (Safiyah Ma)