logo

HAUSA

An kashe a kalla sojojin kasar Kamaru 2 a arewa maso yammacin kasar

2022-08-11 10:33:30 CMG Hausa

Majiyojin rundunar sojojin kasar Kamaru sun ce, a kalla wasu sojojin kasar 2 ne suka rasa rayukansu, sakamakon harin da mayakan ‘yan aware suka kai musu, a yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi dake arewa maso yammacin kasar.

A cewar wasu jami’an rundunar biyu dake yankin da suka bukaci a sakaya sunansu, a ranar Talata ne mayakan ‘yan awaren suka yi wa sojojin kwanton bauna, a karamar hukumar Bamessing da ke yankin, inda suka kashe sojoji biyu nan take tare da raunata wani.

Wasu gungun mayakan ‘yan aware ne suka kai harin, wadanda tun da farko suka samu raunuka a wani harin da sojoji suka kai musu a yankin. (Bello Wang)