logo

HAUSA

Tanzania na fatan Kenya za ta gudanar da babban zabe lami lafiya

2022-08-10 09:36:48 CMG Hausa

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan, ta yi wa makwabtanta al’ummar Kenya, fatan gudanar da babban zaben kasar lami lafiya, yayin da suke kada kuri’a domin zaben shugabanninsu a jiya Talata.

Miliyoyin al’ummar Kenya ne suka kada kuri’unsu a rumfunan zabe 46,229 dake fadin kasar, domin zaben shugaban kasar na 5 da mambobin majalisar dattijai da na wakilai da kuma gwamnonin gundumomi.

William Ruto, mataimakin shugaban kasar mai ci, kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Kenya Kwanza Alliance, ya kada kuri’arsa ne da misalin karfe 6 na safiyar jiya Talata, a wata makarantar firamare dake mahaifarsa wato kauyen Sugoi, dake arewa maso yammacin gundumar Uasin Gishu. Kuma jim kadan bayan kada kuri’ar, ya ce zai girmama sakamakon zaben, wanda aka shafe watanni ana yakin neman zabe mai zafi.

William Ruto na neman takarar shugabancin kasar ne tare da wasu ‘yan takara 3 da suka hada da babba kuma shugaban bangaren masu adawa, Raila Odinga, karkashin jam’iyyar One Kenya Coalition. Shi ma, ya kada kuri’arsa ne a wata rumfar zabe dake Nairobi, babban birnin kasar. (Fa’iza Mustapha)