logo

HAUSA

Jami’an tsaron sun damke wasu mutane 5 da ake zargi da kai wani mummunan hari a wata majami’a a Najeriya

2022-08-10 11:07:12 CMG Hausa

              

Hukumomin Najeriya sun tabbatar da nasarar cafke a kalla mutane biyar, da ake zargi da hannu wajen kai mummunan harin da aka kai a wata majami’a a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin kasar a ranar 5 ga watan Yuni.

Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Lucky Irabor ya shaidawa taron manema labarai jiya a Abuja, babban birnin kasar cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban na kasar.

Shi ma gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akeredolu ya shaidawa manema labarai a wani taron manema labarai na daban da aka shirya jiyan a Akure, babban birnin jihar cewa, baya ga maharan da aka kama, an kuma yi nasarar damke mai gidan da suka sauka kafin su kai harin. .

Akeredolu ya ce, har yanzu jami’an tsaro suna farautar wasu ’yan bindiga da suka kai wannan mummunan hari kan masu ibada da ba su ji ba su gani ba. Yana mai cewa, gwamnati ba ta bata wani lokaci ba, wajen zakulo ’yan ta’addan da ake zargi.

A kalla masu ibada 40 ne rahotanni suka ce sun mutu, wasu 61 kuma suka jikkata, sakamakon harin da aka kai a majami’ar katolika ta St. Francis da ke Owo, a garin Ondo, watanni biyu da suka gabatar. Kuma gwamnatin Najeriya ta ce, tana zargin mayakan IS reshen yammacin Afirka da hannu wajen kai harin. (Ibrahim)