logo

HAUSA

Da Abokin Daka Ake Shan Gari......

2022-08-10 19:19:43 CMG Hausa

Shaidu da abubuwa na zahiri na kara tabbatar da cewa, Sin da Afirka sun zama abin da Malam Bahaushe ke cewa, ’yan uwa rabin jiki”. Duk lokacin da bangaren Sin ya ga abin da zai shafi moriyar kasashen Afirka da ma na kasashe masu tasowa, ya kan yi kokarin ankarar da duniya bukatar kare muradunsu tare da mara musu baya, wajen ganin an cimma burin da ake fata.

Batu na baya-bayan shi ne yadda zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, kuma shugaban kwamitin sulhu na MDD na wannan wata Zhang Jun, ya yi kira ga kasashen duniya, da su goyi bayan Afirka wajen inganta karfinsu na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a cikin kasashensu. Zaman lafiya aka ce ya fi zama dan sarki, kuma sai da zaman lafiya, za a samu duk wani ci gaba da ake fata.

Zhang ya bayyana yayin taron bude muhawarar kwamitin sulhu da kasar Sin ta kira, mai taken "zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka: samar da karfin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa." Tallafin da kasar Sin din ta gabatar sun kasance a fannoni guda 4 ne, wadanda suka hada da karfafa sanin makamar aiki a fannin tafiyar da harkokin gwamnatoci, da inganta kwazon sassan hukumomin tsaro, da bunkasa ikon samar da ci gaba mai dorewa, da renon kwararru.

Jami’in na kasar Sin ya ce, bisa la'akari da irin kwarewar da kasar Sin ta samu wajen samun bunkasuwa, da gogewa daga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma darussan tarihi daga fadin duniya, kasar Sin ta yi imanin cewa, idan har ana son taimakawa Afirka wajen samun kwanciyar hankali na dogon lokaci, wajibi ne a kara zuba jari mai dorewa, da yin tunani mai zurfi, da kuma gina harsashi mai karfi ga Afirka, don kara karfin hanyar samun ci gaba da ta zaba da kanta, da inganta juriyarta kan abubuwan da za su kawo mata cikas daga waje. Sanin kowa ne cewa, sai an zubar da ruwa a kasa kafin a taka damshi.

Saboda muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ci gaban kowa ce kasa a fadin duniya, masu sharhi na kara jaddada cewa, bai kamata a rika gindaya wani sharadi na siyasa da ya shafi samar da taimako ba, kuma bai kamata a rika tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, ko maye gurbin ayyukan da kananan hukumomi suka saba gudanarwa.

Ba abu ne boyayye ba, baya ga kayayyakin more rayuwa da kasashen Afirka suka amfana da su karkashin hadin gwiwar sassan biyu, wato Sin da Afirka. Daga lokaci zuwa lokaci ko dai a taruka ko dandalolin kasa da kasa, bangaren Sin kan yi kokarin kare muradun kasashe masu tasowa baki daya. Abin da ke kara tabbatar da sahihancin alakar sassan biyu. (Ibrahim Yaya)