logo

HAUSA

Tsokacin farfesa Sheriff Ghali Ibrahim kan ziyarar Pelosi a Taiwan

2022-08-09 15:50:33 CMG Hausa

Kwanan nan ne kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi, ta ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin, inda kwararru da masana, da kuma jami’an gwamnatocin kasashe da dama, suka soki lamirin Pelosi kan wannan ziyara, suna masu cewa, ziyarar ta keta hurumin mulkin kai, da kuma cikakkun yankunan kasar Sin, ta kuma sabawa dokoki, gami da ka’idojin kasa da kasa, abun da ya kamata a yi tir da shi.

Taiwan, wani sashi ne na kasar Sin tun shekaru aru-aru da suka gabata. Tun karni na 12, gwamnatin dauloli daban-daban na kasar Sin sun kafa hukumomi a Taiwan, don tafiyar da harkokin mulki. Bayan da kasar Sin ta samu nasara a yakin kin maharan kasar Japan a shekara ta 1945, gwamnatin kasar dake karkashin mulkin jam’iyyar Kuomintang (KMT) a wancan lokaci, ta sake farfado da hukumarta dake lardin Taiwan. Daga baya wato tsakanin shekara ta 1945 zuwa ta 1949, yakin basasa ya barke tsakanin sojojin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da na jam’iyyar KMT, inda jam’iyyar kwaminis ta kasar ta samu nasara, har ya kai ga ta kafa Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a watan Oktoban shekarar 1949, amma ita jam’iyyar KMT ta sha kaye, ta kuma tsere zuwa yankin Taiwan, al’amarin da ya haddasa rabuwar Taiwan da babban yankin kasar Sin na wani kankanin lokaci. Duk da haka, wannan ba zai canja hakikanin gaskiya ba, wato Taiwan, wani bangare ne da ba za’a iya balle shi daga kasar Sin ba.

Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan, bisa hujjar da ta fake da ita, wato “goyon-bayan demokuradiyya”. Amma ainihin makasudin ziyarar ta shi ne, hura wutar kawowa kasar Sin baraka, da keta demokuradiyya, da kuma neman cimma muradun ita kanta, da na jam’iyyar siyasa, gami da na kasar Amurka.

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, darektan cibiyar horas da ‘yan majalisu na jami’ar Abuja, kana masanin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya, ya yi tsokaci kan ziyarar Pelosi a yankin Taiwan na kasar Sin, inda ya ce, har kullum Amurka ta kan yi shisshigi cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, amma ta yi biris da matsalolin kanta, wanda hakan ya sa lokaci ya yi na faduwarta warwas. (Murtala Zhang)