logo

HAUSA

Bincike: Babban iyali da alakar dangi na iya magance cutar mantuwa

2022-08-09 08:32:35 CMG Hausa

Wani sakamakon bincike da kasar Australia ta fitar a kwanakin baya ya nuna cewa, zama a cikin babban iyali da kula da dangantakar dangi na iya rage karuwar matsalar cutar mantuwa.

A cikin wani bincike na kasa da kasa da aka gudanar, wata tawaga daga jami'ar Adelaide ta yi nazari kan sauye-sauye a yanayin rayuwar mutanen da suka haura shekaru 60 daga kasashe da yankuna fiye da 180.

Masu binciken sun gano cewa, mutanen da ke zama a cikin manyan gidaje ko suke tare da iyalai, ba su da hadarin kamuwa ko mutuwa daga cutar mantuwa fiye da wadanda ke zaune su kadai ba tare da la’akari da wasu dalilai kamar shekaru da ci gaban birane ba.

Maciej Henneberg, babban marubucin sakamakon binciken ya bayyana cewa, sakamakon binciken ya tabbatar da cewa, akwai fa'idodi masu kyau ga mutanen da ke zama a cikin al'umma.

Henneberg, ya bayyana a yayin wani taron manema labaru cewa, "A cikin dubban shekaru da suka gabata, muna daya daga cikin 'yan tsirarun da suka dogaro da zama cikin manyan gidaje, sannan kuma suka kulawa da ‘ya’yansu, har sai aka samu ci gaba da wadata a cikin kananan al'ummomi.”

Galibi akwai lokaci da aka tsayar na cin abinci, ana yin tattaunawa, mutane su kan duba don ganin ko kun sha magungunan ku, kuma ’yan uwa suna karfafa yin aiki tare.

"Wannan hadin gwiwa, idan ya dore, yana kara samar da sinadarin oxytocin, wanda galibi ya kan zubarar da sinadarin dake sanya farin ciki, kuma an nuna cewa, yana da kyakkayawan tasiri a kan lafiyar jiki ta hanyar kare yanayin bugun zuciya da jijiyoyin jini da ke hade da ciwon dake da nasaba da jijiyoyin jini, kuma yana iya taimakawa wajen rage kamuwa da cutar mantuwa.”

A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO), fiye da mutane miliyan 55 a duniya suna fama da lalurar mantuwa, inda masu fama da cutar Alzheimer's disease, suka kai kashi 70 cikin 100. Cutar Alzheimer's disease, wani nau’in ciwon karancin basira da dake farawa daga matsalar mantuwa, daga bisani ya shafi tunanin mutane da kwarewar magana har ma da gudanar da harkokin yau da kullum. Cutar ita ce ta 7 a duniya dake haddasa mutuwa kana an yi kiyasin cewa, an kashe kudaden da suka kai dalar Amurka tiriliyan 0.8 kan cutar a duniya.

You Wenpeng, wani mai nazari a kan binciken ya bayyana cewa, sakamakon binciken zai iya yin tasiri matuka kan yadda ake magance cutar mantuwa.

Yana mai cewa, wannan wani muhimmin bincike ne wajen sanar da yadda muke tsara ayyukan kulawa da mutane yayin da suka tsufa, saboda yana nuna cewa, abubuwan da suka shafi dan Adam, da dangantaka, hadin kai da manufa, karfafawa da nuna yabo, hadin gwiwa mai ma'ana da sauransu, duk suna da kyau da muhimmanci wajen yakar ci gaban lalurar mantuwa. (Ibrahim)