logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci a tallafa wa kasashen Afirka don inganta karfinsu

2022-08-09 10:22:25 CMG HAUSA

 

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, kuma shugaban kwamitin sulhu na MDD a wannan wata Zhang Jun, ya yi kira ga kasashen duniya, da su goyi bayan Afirka wajen inganta karfinsu na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a cikin kasashensu.

Zhang ya bayyana haka ne yayin taron bude muhawarar da kasar Sin ta kira, a yayin taron kwamitin sulhu na MDD, mai taken "zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka: samar da karfin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa."

Ya ce, bisa la'akari da irin kwarewar da kasar Sin ta samu wajen samun bunkasuwa, da gogewa daga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma darussan tarihi daga fadin duniya, kasar Sin ta yi imanin cewa, idan har ana son taimakawa Afirka wajen samun kwanciyar hankali na dogon lokaci, wajibi ne a kara zuba jari mai dorewa, da yin tunani mai zurfi, da kuma gina harsashi mai karfi ga Afirka, don kara karfin nahiyar na samun ci gaba da ta zaba da kanta, da inganta juriyarta kan abubuwan da za su kawo mata cikas daga waje.

Ya ce, bai kamata a rika gindaya wani sharadi na siyasa da ya shafi samar da taimako ba, kuma bai kamata a rika tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, ko maye gurbin ayyukan kananan hukumomi suka saba gudanarwa. (Ibrahim Yaya)