logo

HAUSA

BH ta kaddamar da hare-hare a Kamaru

2022-08-09 10:22:52 CMG Hausa

 

Majiyoyin tsaro a kasar Kamaru, sun ce an kashe mutane da dama ciki har da sojoji a karshen mako, sanadiyyar wasu hare-hare da kungiyar Boko Haram ta kai a yankin arewa mai nisa na Kamaru.

Mayakan kungiyar BH sun kai hari kauyen Kismatari na yankin a ranar Lahadi, inda suka kashe fararen hula 3, sannan sun kai wani hari na daban yankin Morgo a ranar da dare har zuwa sanyin safiyar Litinin, inda suka kashe mutum guda da raunata wani na daban.

A ranar Asabar kuma, mayakan sun yi wa wani soja na rundunar hadin gwiwar sojoji ta kasa da kasa, mai suna Olivier Ngono kwantan bauna, inda suka kashe shi.

Wani jami’in yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sojan na kan babur ne a lokacin da mayakan da suka buya cikin daji suka masa kwantan bauna a wani wuri da ake kira da Gogolom, sannan suka bude masa wutar da ta yi sanadin mutuwarsa da matukin babur din da yake kai. (Fa’iza Mustapha)