logo

HAUSA

An bude rumfunan kada kuri’a a babban zaben kasar Kenya

2022-08-09 20:33:24 CMG Hausa

Miliyoyin al’ummar kasar Kenya sun fita rumfunan kada kuri’a, a babban zaben kasar dake gudana a Talatar nan. An dai fara kada kuri’u a babban zaben ne a kimanin rumfuna 46,229, inda ake fatan zaben shugaban kasa na 5 a tarihin kasar, da ‘yan majalissun wakalai, da sanatoci, da kuma gwamnonin gundumomi.

Tun da misalin karfe 6 na safiyar Talatar nan ne mataimakin shugaban kasar mai ci William Ruto, wanda kuma ke takarar shugabancin kasar karkashin gamayyar jam’iyyu na “Kenya Kwanza”, ya kada kuri’ar sa, a mazabar dake makarantar firamaren kauyen Sugoi, a gundumar Uasin Gishu, dake arewa maso yammacin kasar.

Mr. Ruto na fafatawa a zaben na bana ne tare da sauran ‘yan takara 3, ciki har da babban dan hamayyarsa Raila Odinga, wanda tsohon jagoran ‘yan adawa ne, da a yanzu ke takarar shugabancin kasar karkashin gamayyar “Azimio La Umoja”.

Sauran ‘yan takarar sun hada da George Wajackoya, masanin shari’a wanda ke takara karkashin jami’iyyar “Roots”, da kuma David Waihiga, tsohon dan siyasa dake takara karkashin jami’iyyar Agano. (Saminu Alhassan)